Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama bakin haure 12 ‘yan kasashen Mali da Jamhuriyyar Nijar da suka shigo Najeriya ba tare da izini ba.
‘Yan sandan sun kuma kama masu aikata laifuka daban-daban 33 a fadin jihar.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar Mohammed Usaini-Gumel ya sanar da haka ranar Laraba da yake ganawa da manema labarai a garin Kano.
“ Mutanen da suka shigo kasar nan ba tare da izini ba sun gudu ne daga Saudiyya sannan suka boye a wani gida dake kwatas din Hotoro Yandodo a Kano.
“Mun ga mutanen da rauni a yatsun su.
“Mun kama bata gari da suka hada da suka hada da barayi, ‘Yan fashi da makami, rike da amfani da bindiga ba tare da izini ba da dai sauran su.
“An kama wadannan mutane da wayoyin hannu 46, layin wayar 21, wukake, addunan, bindigar roba, makullai, ledan kwayoyin Diazepam, kwayoyin exol guda 79 da busasshen ganyen da ake zargin wiwi ne da dai sauran su.
Usaini-Gumel ya ce idan rundunar ta kammala bincike za ta maka wadannan mutane kotu domin yanke musu hukunci.
Ya yi kira ga jami’an tsaron da su kara zage damtse wajen ganin sun rage muggan aiyukka a jihar.
Usaini-Gumel ya kara yin kira ga mutane da su ci gaba da mara wa jami’an tsaro baya a fadin jihar.
Discussion about this post