Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta bayyana cewa wasu mahara da ake zargin ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da daliban jami’yyar Jos bakwai.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Alfred Alabo ya sanar da haka da yake zantawa da manema labarai ranar Laraba a garin Jos.
Alabo ya ce maharan sun yi garkuwa da daliban lokacin da suke karatun jarabawar da aka fara ranar Talata a dakunan su na kwana dake kusa da Jami’ar a cikin dare.
“Maharan sun yi garkuwa da daliban da misalin karfe 8:30 na daren Litini a gidan da suke zama dake Bauchi road a karamar hukumar Jos ta Arewa.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bartholomew Onyeka ya Bada umarnin gudanar da bincike domin kamo maharan tare da ceto wadanda aka yi garkuwa da su cikin koshin lafiya.
“Rundunar Operation Safe Haven tare da sauran jami’an tsaron jihar za su hada hannu domin ceto daliban da aka yi garkuwa da su.
Rundunar ta yi kira ga mutane da su kwantar da hankulan su cewa rundunar za ta yi kokari wajen ceto daliban tare da kamo maharan da suka yi garkuwa dasu.
Discussion about this post