‘Yan bindiga a daren Lahadi sun kashe shugaban ‘yan banga Mallam Nabanje sannan suka kona gidansa dake karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina.
Mutum biyu sun ji raunin harsashi a jikinsu sannan maharan sun yi garkuwa da mata uku inda suka sake su bayan sun yi musu fyade,
Wani mazaunin kauyen mai suna Murtala ya bayyana wa ‘ jaridar Vanguard’ cewa maharan sun kawo wa kauyen hari ne domin su kashe Nabanje.
Ya ce maharan sun kashe Nabanje ne saboda a baya ya sanar wa jami’an tsaro bayanna sirri game da inda suke boye a Dan Musa, suka babbake musu wuaren boyar su.
“ Maharan sun gano Nabanje a karkashin Wani bishiya dake cikin gidansa sai ya gudu ya shiga wani gini.
“Daga nan ne maharan suka yi wa ginin zobe suka yi wa Nabanje yankan rago sannan suka banka wa gidansa wuta.
Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandar jihar Sadiq Abubakar ya tabbatar da aukuwar haka sannan ya ce rundunar bata samu labarin abin da ya faru ba sai da karfe 6 na safiyar Litini.
Ya ce hakan ya faru ne saboda ruwan saman da aka kwana ana yi da ya sa aka kasa aika wa jami’an tsaro sako.
Abubakar ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo maharan da suka aikata wannan mummunar abu.
Discussion about this post