A karamar hukumar Rafi jihar Neja ne ‘yan bindiga suka yi garkuwa da mata da ‘yan mata da dama bayan sun kashe manoma 25 a wasu kauyukan dake jihar.
Wannan abin tashin haukali ne a ranar Juma’ar makon jiya a kauyuka biyar.
Wani basarake a karamar hukumar da baya so a fadi sunnan sa saboda tsaro ya ce ‘yan bindiga sun ci gaba da kai wa kauyukan yankinsu hari a cikin makonni biyu da suka gabata.
Sanatan dake wakiltar Neja ta Gabas Mohammed Musa ya koka da yadda a cikin kwanakin da suka gabata ‘yan bindiga ke yawan kai wa kananan hukumomin Rafi, Paikoro, Munya da Shiroro hari.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Wasiu Abiodun ya ce rundunar ta aika da jami’anta zuwa kauyukan Yakila, Tegina, Kagara, Pandogari, Kusherki da sauran kauyukan dake yankin domin Samar da tsaro.
Discussion about this post