‘Yan bindiga sun kashe Ardon Birni da Kewaye na masarautar Zazzau Shuaibu Mohammed da ‘ya’yan sa hudu.
Wannan abin tashin hankali ya auku ne ranar Asabar da karfe 10 na dare a kauyen Dorayi dake karamar hukumar Zaria jihar Kaduna.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ya rawaito cewa bayan kashe Ardo Shu’aibu da maharan suka yi, sun sace masa shanu sama da 100.
Matar Ardo, Halima Shuaibu ta bayyana cewa a goshi suka dirka wa mijin ta Ardo Shu’aibu bindiga, daga bisani kuma suka bi daki daki ida yayan sa ke tare da matan su suka kashe daya bayan daya.
“ Maharan sun kashe Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da Ibrahim Haruna. Sanna kuma suka kora shanun sa sama da 100 suka tafi da su.
Daya daga cikin ‘ya’yan Ardo da maharan suka harba Kuma ya tsira da ransa Abdurrahman Shuaibu ya ce maharan sun harbe wasu mutum biyu kafin suka fice daga kauyen.
Wani mazaunin kauyen Tanimu Haske ya ce ga dukan alamu maharan sun zo musamman domin su kashe Ardo da ‘ya’yan sa saboda yana da kudi.
Discussion about this post