Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da ƙwato bargar motoci har 40 daga gidan tsohon Gwamna, Bello Matawalle.
PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa zaratan ‘yan sanda sun kewaye gidajen Matawalle biyu da ke Gusau da kuma Maradun a safiyar Juma’a.
Kakakin Gwamnan Zamfara, Idris Sulaiman Bala, a cikin wata sanarwa ya Gwamnatin Jihar Zamfara ta aika wa Matawalle saƙon cewa ya maida dukkan motocin da ya kwashe mallakar gwamnatin jihar, a cikin kwanaki biyar, amma ya yi ƙemadagas, ya ƙi maidawa.
Ya ce Rundunar ‘Yan Sandan Zamfara ta yi aiki ne bisa umarnin da wata kotu ta bayar, tare da sammacin amincewa ‘yan sanda su je su ƙwato motocin.
“Idan ba a manta ba, gwamnatin jihar Zamfara ta ta aika wa tsohon Gwamna Matawalle wasiƙa bisa tsari cewa shi da Mataimakin sa su maida dukkan kadarorin motocin da su ka kwashe a cikin kwanaki biyar.
“Mun kuma rubuta ƙorafi zuwa ga ‘yan sanda dangane da kwasar kadarorin gwamnati da su Matawalle su ka riƙa yi, har da motoci masu yawa.
“Daga nan ‘yan sanda su ka nemi sammacin watannin kotu, sannan su ka afka cikin gidan Matawalle da ke Gusau da Maradun, da kuma wani gidan na sa da ke wani wuri a ɓoye.
“An samu motoci 40 ciki har da masu sulken hana shigar harsasai huda ta guda uku, sai SUV takwas.” Inji Idris.
Sai dai kuma APC Reshen Zamfara ta ce kintsawar da gwamnatin Dauda Lawal ta Zamfara ta sa aka yi a gidan Matawalle, hauka ne da dabbanci.
Kada a manta, kusa da saukar sa, EFCC ta fara binciken yadda Matawalle ya yi walle-walle da naira biliyan 70 daga asusun Zamfara
Discussion about this post