Wasu mahara da ake zargi ƴan Boko Haram sun yi wa manoma 7 yankan rago a Maiduguri jihar Borno ranar Alhamis.
Maharan sun dira wa manoman a lokacin da suke aiki a gonakinsu a kauyen Molai dake da nisan kilomita biyar daga Maiduguri.
Tsohon kwamishinan matasa da Wasanni Kuma Shugaban jami’an tsaron dake samar da tsaro wa manoma Sainna Buba ya tabbatar da haka wa PREMIUM TIMES.
Buba ya ce an yi jana’izar wadannan manoma ranar Juma’a bisa ga koyarwar addinin Musulunci.
Wani jami’in tsaro na Civilian-JTF Abudulmumeen Bulama ya ce wani cikin manoman da maharan suka kai wa harin ya gudu ya tsira da harbin bindiga.
“ Ko da muka isa wurin, mun iske wasu daga cikin waɗanda aka kashe an yi musu yankan rago ne kawunan su a kasa.
Ya ce kisan da maharan suka yi ya tsorata manoman a yankin.
Discussion about this post