‘Yan bindiga a ranar Asabar din da ta gabata sun kashe Wani babban dan kasuwa sannan sun yi garkuwa da wasu mutane uku da a cikinsu akwai dagacen garin Bakutunbe da hakimim Balma, karamar hukumar Ningi.
Shugaban karamar hukumar Ningi Ibrahim Zubairu ya ce maharan sun Yi garkuwa da hakimin Balma Hussain Saleh da dagacen Bakutunbe Idris Mai Unguwa sannan sun kashe Wani babban dan kasuwa Haruna Dan-Oc.
Wani mazaunin Balma dake da baya so a fadi sunnan sa ya ce maharan sun tafi da hakimin da karfe 11 na dare.
” Da suka shiga kauyen sai suka nufi didan hakimin suna ta ɓarin wuta da bindigogin su. Da ga nan ne mutane suka arce kowa yayi ta kansa.
A wannan dare ‘yan bindigan sun afka kauyen Bakutunbe suka yi garkuwa da dagacen kauyen da wani Ya’u Gandu mai shekara 45.
Maharan na yi wa kowannen su kuɗi kan Naira miliyan 8 kuɗin fansa.
Discussion about this post