Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu alaikum,
Allahu Akbar!
‘Yan uwana ‘yan Najeriya, a gaskiya ko yanzu ‘yar manuniya ta nuna, cewa lallai wajibi ne kowa yayi kokari yaga cewa ya zamo mutumin kirki, nagari, mai mutunci, mai kishin kasar sa da al’ummarsa da gaske. Wannan zai sa ka zamo abun so da kauna ga kowa da kowa.
Abun da yasa nace haka kuwa shine: yau a wannan rana ta Alhamis, 15/06/2023, wallahi duk mai bibiyar abubuwan da suke faruwa a social media, da sauran kafafen yada labaran kasar nan, game da lamurran kasar mu mai albarka wato Nigeria, lallai yaga wani abun mamaki kwarai da gaske, wanda zai burge duk wani mai kishin kasarsa da son ci gaban ta.
Yau din nan, wata ganawa da tattaunawa ta faru, tsakanin mai girma shugaban kasar Nigeria, wato Alhaji Bola Ahmad Tinubu da Mai Martaba Sarkin Kano na 14th, wato Khalifah Muhammad Sanusi II, a fadar gwamnatin kasa; wanda ganawar ke da wuya, wallahi sai kasar nan baki daya ta dau harama, da murna da farin ciki da jin dadi.
Kowa yana ta fadin albarkacin bakinsa, tare da nuna kyakkyawan fatan alkhairi game da wannan muhimmiyar ganawa mai cike da dimbin tarihi.
Ni dai na bibiyi dukkanin labarai game da wannan ganawa, amma wallahi ban ga wani mutum guda mai fadin wata magana marar dadi ba.
Sannan wallahi kowa sai murna yake yi, yana yabawa shugaba Tinubu, wanda alamu suke nuna lallai shi mutum ne mai sauraron al’ummah, kuma lallai ya nuna yana son ci gaban kasar nan da gaske, domin ta bayyana a fili cewa, shi da masu ilimi zai yi aiki domin ceto kasar nan da izinin Allah, daga halin da take ciki.
Shi kuma Khalifah Muhammad Sanusi II, wallahi yau yasha kyawawan addu’o’i da fatan alkhairi daga wurin ‘yan Najeriya.
Wannan shine dalilin da yasa nace lallai mutum ya zamanto nagari, to akwai alkhairi mai tarin yawa tattare da hakan.
Kuma lallai shi hakuri da mayar da lamari ga Allah, ba karamin abu bane.
Mutane zasu ga sun zalunceka, sun cuce ka, sun ci mutuncinka, amma idan kayi hakuri, ka mayar da lamarinka ga Allah, sai Allah yayi maka sakayya ta inda baka yi tsammani ba.
Duk da bamu san me aka tattauna a wannan muhimmiyar ganawa ba, amma dai mun san da ikon Allah, wannan ganawa alkhairi ce ga kasar mu Nigeria.
Ina addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala yasa wannan ganawa ta amfani kasar mu, amin.
Shugaba Tinubu da Mai Martaba Sarki, ina addu’a da rokon Allah yayi masu jagora, amin.
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, Alhamis, 15/06/2023.
Discussion about this post