Gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani ya nada tsohon kwamishinan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan, Kantoman Hukumar Birnin Kaduna da Kewaye.
Sanarwar nadin na kunshe ne a wata takarda wacce Sakataren yada labarai na gwamnan jihar Mohammed Shehu ya fitar ranar Talata.
Gwamna Sani ya yi masa fatan alkhairi tare da yin kira a gare shi da ya yi amfani da kwarewar sa wajen kawo sauye sauye masu ma’ana a jihar da kuma ci gaban Babban Birnin jihar da kewaye.
Discussion about this post