Gwamnan jihar Kaduna ya naɗa sabbin mashawarta 14 ciki har da tsohon ɗan majalisar tarayya, Sama’ila Suleiman wanda ɗan tsohon gwamnan jihar Bello El-Rufai ya kada a zaɓen majalisar wakilai a zaɓen 2023.
Idan ba a manta ba, ba a ga maciji tsakanin Samaila Suleiman da tsohon gwamna Nasir El-Rufai in da ya rika sukar sa ya na masa izgilanci da kurin sai ya kada ɗan sa Bello a takarar.
Sai dai kuma bayan zaɓen da aka yi, dara ta canja gida, Samaila ya tattara kayan sa ya watsar da jam’iyyar PDP ya koma APC inda aka san shi a baya.
Sakamakon haka, ya sa gwamnan jihar, Uba Sanibya saka masa da mukamin mashawarci.
Ga sauran wanda aka naɗa a nan:
1. Dr. Abdul Ishaq – Stakeholders Relations
2. Atiku Sankey – Peace and Conflict Resolution
3. Dr. Daniel Manzo Maigari – Political Affairs
4. Ibrahim T. Muhammad – Economic Matters
5. Dr. Mustapha Musa – Legal Matters
6. Fabian Okoye – Research, Documentation & Strategy
7. Dr. Abdullahi B. Ahmed – Project Monitoring, Implementation and Result Delivery
8.Mary Adeola Olarerin – Programme Monitoring & Evaluation
9. Sagir Balarabe Musa – Human Capital Development
10. Muktar Ibrahim – Chieftaincy Matters
11. Sabiu Sani – Investment & Promotion
12. Bridget A.O. Sulaiman – Social Investment Programme
13. Dr. Abdulkareem Mayere – Energy
14. Samaila Suleiman – Counselor, Infrastructure
Discussion about this post