Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Paris na ƙasar Faransa, domin halartar Taron Yarjejeniyar Bunƙasa Tattalin Arziki na Global Financing Pact Summit’, wanda Shugaba Emmanual Macron na ƙasar ya shirya.
Ya isa filin jirgin saman Paris, inda Jakadan Najeriya a Faransa, Kayode Laro ya tarbe shi.
Za a yi taron na kwanaki biyu a ranakun 22 da 23 Ga Yuni.
Zai kuma gana da shugabannin ƙasashen duniya, domin tattauna hanyoyin da za a dawo da martabar yanayi da hana gurɓacewar sa, sai kuma batun farfaɗo da tattalin arziki, wanda ya taɓarɓare tun bayan ɓullar korona.
Tinubu ya tafi, kwana ɗaya bayan ya rusa wasu Hukumomin Gudanarwar da haɗa da NUC, JAMB, NECO, TETFund, UBEC da wasu birjik.
Discussion about this post