‘Yan bindiga sun waske da wasu mata biyu ‘yan jami’yyar APC daga karamar hukumar Birnin Gwari jihar Kaduna ranar Talata.
Shugaban kungiyar Birnin Gwari Emirate Progressive Union (BEPU), Ishaq Kasai ya sanar da haka wa manema labarai ranar Laraba.
Kasai ya ce maharan sun yi awon gaba da wadannan mata a Manini yayin da suke hanyar su ta dawowa daga taron rantsar da sabon gwamnan jihar Kaduna Uba Sani da aka yi a garin Kaduna.
Ya ce maharan sun tare hanya inda suka sace matan biyu da ‘yan jam’iyyar APC ne tare da matafiya da dama.
Wadanda aka sace sun hada da Lami Awarware da mai taimakamata Haulatu Aliyu.
Zuwa yanzu dai maharan basu kira ‘yan uwan wadanda suka yi garkuwa da su ba.
Zuwa lokacin da aka rubuta wannan labari kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Muhammed Jalige bai ce komai ba.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin yankin Arewacin Najeriya dake fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Gwamnatin jihar a karkashin jagorancin tsohon Nasir El-Rufa’I ta dauki matakai da dama domin kawo karshen hareharen maharan a jihar.
Shima Uba Sani ya yi alkawarin kawo karshen wannan harehare musamman a yankunan Kaduna ta tsakiya da ta kudu.
A cikin jawabin sa ya ce ba zaiyi kasa a guiwa ba wajen ganin gwamnati ta kirkiro yan sandan jihohi.
Discussion about this post