Idan ba a manta ba, Iyan Zazzau, Tajudeen Abbas ne ya yi nasara a zaɓen shugaban majalisar wakilai ta tarayya, inda ya doke abokanan takarar sa Jaji da Wase a zaɓen shugaban majalisan.
Sai dai kuma a lokacin da ake rantsar da sabon kakain majalisan, matanshi biyu suka nemi kaurewa da faɗa a idanun duniya.
Honarabul Abbas ya shan rantsuwa kenan tare da shi da mataimakin akawun majalisar wakilai da Amaryarsa da Ado Doguwa wanda ya raka Abbas can sama wurin kujerar Kakakin majalisan, sai uwargidan sa ta haura sama ita ma.
Ɗaya daga cikin matan kakakin ta kutsa, ta ratsa daruruwan maza da ke cike makin a zauren majalisa, ta haura sama inda ake rantsar da Honarabul Abbas, ta bangaje Amaryar, ta rika surfa wa masa maganganu duniya na kallo, ita ma ta tsaya cak sai anyi rantsuwar da ita.
Sai dai duk da haka, abin da ta yi bai hana a ci gaba da rantsuwar ba, sai dai kawai matar gida sai ta koma gefen hagu, aka ci gaba da abinda ake yi.
Mutane da dama da suka halarci wannan wuri da waɗanda suka kalli abin a kwatinan talbijin sun yi tir da abinda matan suka yi da irin tozarta mijin su da suka ya idanun duniya.
” Koma dai menene ke tsakanin su, a dai iya bari a koma gida tukunna, amma ba a wuri irin majalisar tarayya ba, shine fa mutum na hudu a kasar nan, amma matarsa ta yi masa irin wannan tonon asiri haka. Bata kyauta ba.
” A nawa ra’ayin, da ma bai zo da ko daya daga cikin su ba kawai. Amma wannan tabon har abada ne ne fa. Kowa ya ga irin halin matarsa a duniya. Gaskiya ba su kyauta masa ba.
Discussion about this post