Shugaba Bola Tinubu ya rushe dukkan shugabannin hukumomin gwamnati, na ma’aikatu da na cibiyoyi da na kamfanonin gwamnatin tarayya.
Amma sanarwar ta ce ba a rushe Hukumomi da Majalisu na Gwamnatin Tarayya da Sashe na 1 a Ɓangare na 153 (1) na Dokar 1999 ba.
Wannan sanarwa ta na ƙunshe ne a bayanan ranar Litinin, wanda Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar.
An umarci shugabannin hukumomin su damƙa kayan bayanai a Ofishin Babban Sakataren Ma’aikatun da su ke ƙarƙashin su.
Wannan umarni ya fara ne daga ranar 16 Ga Yuni, 2023.
PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Tinubu ya kori manyan hafsoshin tsaro, Shugaban ‘Yan Sanda da na Kwastan, ya naɗa Ribadu Mashawarcin Tsaron Ƙasa
ASHAFA MURNAI
Shugaba Bola Tinubu ya kori dukkan Manyan Hafsoshin Tsaro da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda da Mashawarta da Shugaban Hukumar Kwastan.
Korar ta haɗa da yi masu ritaya, sannan kuma ya nada sabbi nan take.
Sabbin da ya naɗa sun haɗa da:
1 Malam Nuhu Ribadu – Mashawarcin Shugaban Ƙasa a Harkokin Tsaro.
2 Maj. Gen. C.G Musa – Babban Hafsan Tsaron Ƙasa.
3 Maj. T. A Lagbaja – Babban Hafsan Askarawan Najeriya.
4 Rear Admirral E. A Ogalla – Babban Hafsan Sojojin Ruwa.
5 AVM H.B Abubakar – Hafsan Sojojin Sama.
6 DIG Kayode Egbetokun – Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, na Riko.
7 Maj. Gen. EPA Undiandeye – Babban Hafsan Leƙen Asiri.
Haka kuma Shugaba Tinubu ya amince da naɗa:
1 Col. Adebisi Onasanya – Babban Kwamandan Dakarun Tsaron Shugaban Ƙasa (Brigade of Guards).
2 Lt. Col. Moshood Abiodun Yusuf – Babban Dakaren 7 Guards Battalion, Asokoro, Abuja).
3 Lt. Col. Auwalu Baba Inuwa – Babban Dakaren 177, Guards Battalion, Keffi, Nasarawa State.
4 Lt. Col. Mohammed J. Abdulkarim – Babban Dakaren 102 Guards Battalion, Suleja, Niger.
5 Lt. Col. Olumide A. Akingbesote – Babban 176 Guards Battalion, Gwagwalada, Abuja.
Sauran sun haɗa da:
1 Maj. Isa Farouk Audu
(N/14695) – Kwamandan Sojojin Atilare na Fadar Shugaban Ƙasa.
2 Capt. Kazeem Olalekan Sunmonu (N/16183) – Mataimakin Kwamandan State House Artillery.
3 Maj. Kamaru Koyejo Hamzat (N/14656) – Commanding Officer, State House Military Intelligence.
4 Maj. TS Adeola (N/12860) Commanding Officer, State House Armament.
5 Lt. A. Aminu (N/18578) – Mataimaki State House Armament.
Sai kuma ƙarin mashawartan musamman huɗu:
1 Hadiza Bala Usman a Fannin Tsare-tsare.
2 Hannatu Musa Musawa – a kan Al’adu.
3 Sen. Abdullahi Abubakar Gumel – Mashawarcin Musamman kan Majalisar Dattawa.
4 Hon. (Barr) Olarewaju Kunle Ibrahim – Masahawarci na Musamman a Majalisar Tarayya.
Adeniyi Bashir Adewale kuwa an naɗa shi Shugaban Riƙon Hukumar Kwastan.
Discussion about this post