Shugaba Bola Tinubu ya rattaba hannun maida Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA) da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) a ƙarƙashin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.
Ya maida su ne kamar yadda dokar Najeriya ta ce a can za su kasance tun farkon kafa su.
Daraktan Yaɗa Labaran Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Olusola Abiola ne ya fitar da wannan sanarwar a ranar Talata.
Dama kuma a cikin wata sanarwar Tinubu ya ce Hukumomin biyu ba su cikin waɗanda aka rushe.
Hukumomin Gudanarwar da Tinubu ya rusa sun haɗa da NUC, JAMB, NECO, TETFund, UBEC da wasu birjik.
Hukumomin Gudanarwar da Tinubu ya rusa sun haɗa da na jami’o’i, Kwalejojin Fasaha, JAMB, NUC da dukkan hukumomin da ke ƙarƙashin Ma’aikatar ilmi.
Akwai NBAIS, NERDC, NMEC, NECO, LRCN, NBTE, NCCE, UBEC, CPN, TETFund, NABTEB, NTI, NINLAN, TRCN da sauran su.
Akwai kuma wasu Hukumomi 14 Waɗanda Tinubu bai rusa da guduma.
Akwai Hukumomi 14 waɗanda Tinubu bai rusa da guduma ba.
1. Hukumar Gudanarwar Lafafta Ma’aikata (CCB), wato Code of Conduct Bureau.
2. Majalisar Gudanarwa.
3. Hukumar Federal Character Commission.
4. Hukumar Ma’aikata ta Tarayya.
5. Hukumar Kula da Alkalai ta Ƙasa.
6. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC.
7. Majalisar Tsaro ta Ƙasa.
8. Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa.
9. Majalisar Shari’a ta Ƙasa.
10. Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa.
11. Majalisar Harkokin Tsaro ta Ƙasa.
12. Hukumar Aikin ‘Yan Sanda ta Ƙasa.
13. Hukumar Ɗaukar ‘Yan Sanda ta Ƙasa.
14. Hukumar Rarraba Kuɗaɗen Shiga Ga Sassan Gwamnati.
Discussion about this post