Shugaba Bola Tinubu bai amince da karin albashi ga masu rike da mukaman siyasa da na shari’a ba, in ji kakakin.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Dele Alake, yana mayar da martani ne ga wata sanarwa da wani jami’in hukumar (RMAFC) ya yi cewa an amince da karin albashin kashi 114 ga masu rike da mukaman siyasa.
Sai dai kuma Alake bai musanta cewa RMAFC ta yi irin wannan shawara ba amma ya ce ba za ta iya aiki ba sai shugaban kasa ya amince da shi.
” Eh, duk da doka ta baiwa hukumar RMAFC damar tsara albashin masu rike da mukaman siyasa, ba zai tabbata ba sai dole shugaban kasa ya rattaba hannu a kai sannan hakan zai iya fara aiki.
Discussion about this post