Lodi da tulin ɗanyen man Najeriya ya fara kwantai a duniya, saboda rashin zaburowar masu saye daga Chana, ƙasashen Turai da kuma Indiya.
Lamarin maras daɗin ji na faruwa ne yayin da waɗannan ƙasashen da aka lissafa su ka juya wa ɗanyen man Najeriya, su ka koma sayen mai arha tiɓis daga Rasha.
Maida hankali da masu sayen ɗanyen mai kan na Rasha, samfurin Urals, ya samar masu rage kashe maƙudan kuɗaɗen da su ke yi wajen sayen ɗanyen mai wanda ke da tsada.
Gingima-gingiman jiragen ruwa ɗauke da ɗanyen mai daga Najeriya na can bakin tekun tashoshin jiragen ruwan ƙasashe a tsaitsaye, babu isassun masu sayen mai.
Shi dai ɗanyen man Najeriya wanda samfuri iri uku ne, wato Bonny K
Light’, Forcados’ da ‘Brass’, su na da daraja a duniya ne saboda sinadarin salfurik ɗin cikin sa ba mai kauri ba ne. Kuma hakan Turai da ƙasashen Asiya su ka fi son ɗanyen mai ya kasance.
Sai dai kuma kasuwa ta yi juyi yanzu kwastomomin Najeriya sun fara karkata zuwa ga samfurin ‘Urals’ daga Rasha, saboda a ganin su, na Najeriya ya yi tsada sosai.
Wannan jawabi da bincike ya fito ne daga Cibiyar Nazarin Farashin Kaya ta Duniya, S&P Global Commodity Insights.
A yanzu haka sun kai ga ana yin ragin senti 50 a duk ganga ɗaya ta ɗanyen man Najeriya, samfurin Bonny.
Haka shi ma ɗanyen mai Brazil an ɗan rage masa farashi, shi ya sa kasuwar ga gangar ɗanyen man Najeriya ta yi kwantai a Turai.
Wannan lamari ya ƙara dagula matsalolin da Najeriya ke ciki, inda ya yanzu yawan ɗanyen mai da Najeriya ke haƙowa ya yi baya sosai, kusan shekaru goma rabon da a riƙa haƙo adadin wanda ake haƙowa mai ƙaranci a yanzu.
Ɗanyen mai da Najeriya ke haƙowa a kullum yanzu bai kai ganga miliyan 1 ba, maimakon ganga miliyan 2.2 da ya kamata ta riƙa haƙowa a kullum. Ga shi kuma ana fama da ɓarayin ɗanyen mai, waɗanda su ka haifar wa gwamnatin tarayya asarar dala biliyan 1 daga Janairu zuwa ƙarshen Maris.
Discussion about this post