A cikin kwanaki biyar zuwa yau, mazauna wasu yankunan Zamfara da Sokoto sun ɗanɗana bala’in hare-haren ‘yan bindiga.
Wasu da Allah ya kuɓutar daga hannun waɗannan ‘yan ta’adda, sun bayyana cewa maharan su na matsa-ƙaimin kai hare-haren don kawai sabbin gwamnoni su neme su a yi sulhu da su.
A ranar 29 Ga Mayu, an rantsar da dukkan gwamnoni bakwai na sabbi na jihohin Arewa maso Gabas da kuma Neja a tsakiyar Najeriya, waɗanda su ne jihohin da ‘yan bindiga su ka fi yi wa mummunar ɓarna.
Wasu tsoffin gwamnoni a waɗannan jihohi, kamar Aminu Masari a Katsina, Abdul’aziz Yari da Bello Matawalle na Zamfara duk sun taɓa yin sulhu da ‘yan bindiga a jihohin su.
Sai dai kuma ko sun ƙulla yarjejeniyar ba ta ƙarƙo, sai ‘yan ta’adda su ci gaba da kai hare-hare kan hanya da kuma cikin ƙauyuka da garuruwa su na garkuwa da mutane da mummunan kisa.
PREMIUM TIMES ta yi magana da mutum biyu waɗanda aka taɓa yin garkuwa da su a Zamfara. Sun shaida masa cewa waɗannan sabbin hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa, su na yi ne don sabbin gwamnoni su nemi a yi sulhu da su.
“A lokacin da mu ke hannun ‘yan bindiga, mun sha ji sau da yawa su na magana cewa za su ƙara ƙaimin kai hare-hare, domin su tilasta wa sabbin gwamnoni su saurare su.” Haka wani mai shekaru 37, kuma ɗan tireda da ke ƙauyen Katuru ya shaida wa wakilin mu.
Mutumin wanda ya nemi a ɓoye sunan sa, saboda tsoron abin da ka iya faruwa da shi, ya ce ‘yan ta’addar da su ka yi garkuwa da shi sun kasance a ƙarƙashin Bello Turji ne.
Wani shi ma da aka taɓa yin garkuwa da shi ɗin a kwanakin nan, amma ya kubuta, ya ce gogarman ‘yan bindigar da su ka yi garkuwa da shi ya taɓa hukunta wasu yaran sa biyu saboda haushin sun yi garkuwa da “ƙaramar yarinya”, maimakon su je su karkashe manya su na garkuwa da waɗanda za su samu maƙudan kuɗaɗe a hannun su.
“Wallahi na ji su na cewa su ƙyale ni kawai na tafi. Ya ce shi ya na so su kashe manyan mutane da yawa. Su kuma kama manyan masu mulki, ta yadda gwamnati za ta san cewa lallai da gaske su ke yi.
“Ya ce idan gwamna da gaske ya ke yi, to zai kira su da kansa domin ya ji buƙatun su, domin su ma ‘yan jihar ne kamar kowa.”
“Aka sace ni aka tafi da ni har bakin hanya, su kuma ‘yan uwa na aka yi gaba da su. Sai da iyayen mu su ka biya kuɗin fansa.
Haka yarinyar mai shekaru 24 da a yanzu ke zaune wurin kawun ta a Talata Mafara ta shaida wa PREMIUM TIMES ta wayar tarho.
Wani mai yi wa jama’ar karkara hidima mai suna Buhari Moriki, ya ce wannan magana ta ‘yan bindiga za ta iya zama gaskiya.
Ya ce shi dai ya na goyon bayan zaunawa da ‘yan bindiga, amma a kan sharuɗɗa biyu.
“Na farko dai a tabbatar sharaɗin farko idan za a sasanta, to su yarda a karɓe dukkan makaman su. Sannan kuma kada a ba su kuɗi.
An tuntuɓi jami’in yaɗa labaran Gwamnan Zamfara, Mustapha Jafaru Kaura, wanda ya ce Gwamnatin Jihar Zamfara ba ta da masaniyar wannan rahoto.
Discussion about this post