Tsohon Sanata Adamu Bulkachuwa, ya fito a karon farko ya ce ko sau ɗaya bai taɓa ribbatar matar sa tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Ƙara ta kauce shari’a don ta hukuncin da ya ke so a kotu ba.
Zainab ce Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara tsakanin 2014 zuwa 2020.
An ruwaito Bulkachuwa ya yi kasassaɓar cewa ya sha neman alfarma ga abokan sa ‘yan siyasa a wajen matar ta sa Zainab, kuma ta na biya masa bukatun alfarmar.
Wannan kasassaɓar dai ta ƙara sa jama’a da dama sun ƙara ɗora karan-tsana kan ɓangaren Shari’a.
Shi dai Bulkachuwa ya ce tsohon Shugaban Majalisar Dattawa bai bari ya ƙarasa bayyana abin da zai ce ba.
Ya ce matar sa na taimakawa ta fannin shawarwari ba ta hanyar yi masu alfarma ba a Shari’a.
Yayin da Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, Yakubu Maikyau ya ce furucin sanatan cin fuska ne ga fannin Shari’a, shi kuwa tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa, Olisa Agbakoba, kira ya yi a kama Bulkachuwa da Zainab a tuhume su.
Discussion about this post