Gazagurun tsohon ɗan tawaye, Asari Dokubo, ya ce Sojojin Ƙasa da Sojojin Ruwan Najeriya ne manyan ɓarayin ɗanyen mai a Neja Delta.
Ansari ya yi wannan kakkausan zargi ranar Juma’a, lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu.
Ya ce fadar ne domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu.
“Sojojin Najeriya na Ƙasa da na Ruwa ne manyan ɓarayin ɗanyen mai a yankin Neja Delta. Su na firgita jami’an Sibil Defens waɗanda su ne ke tsaron wuraren ɗanyen mai. Ta kai ma kai tsaye su ke ɗaura bututu su riƙa zuƙa daga famfon ɗanyen mai.
“Abin da ke faruwa tsawon shekaru takwas kenan ya wuce hankali a duniyar nan. Babu inda aka taɓa yin gagarimar satar ɗanyen mai irin wannan ba a duniya.” Cewar sa.
“Sojojin Sama da na Ƙasa da aka tura don su samar da tsaro, su ne satar ɗanye mai har ta kai sun kafa wuraren tace mai. Haka kuma wannan laifi ne babba.
“Muhallin yankin na ci gaba da gurɓata. Kuma sojojin ƙasa da na ruwa su ne masu aikata wannan babban laifi.
Akwai wasu hatsabiban kwamandojin soja waɗanda ke sahun gaba wajen satar mai.
Ya ce amma yanzu zuwan Bola Tinubu da kuma ƙwarin guiwar da sabon shugaban ya ba shi, za a kakkaɓe sace-sacen ɗanyen mai a Neja Delta.
“Akwai wasu manya a Abuja masu hannu a satar mai. Amma zamanin Tinubu duk za a damƙe su, a maka kurkukun Kuje.”
Discussion about this post