Bari a fara da tuna wa mai karatu lokacin da mutane su ka riƙa yin tururuwa a ciki watan Janairu, 2012 su na zanga-zangar rashin goyon bayan cire tallafin mai. A wancan lokacin maganar gaskiya mutane akasari ba su da masaniyar ma abin da ake nufi da tallafin fetur da kuma asarƙala da sabarƙalar da ke cushe a cikin tsarin.
Da ya ke tsarin biyan tallafin fetur abu ne mai cike da kwatagwangwama, gidoga da baranƙyanƙyamar harƙalla, sai ya kasance su waɗanda su ka fahimci ma’ana da kuma dalilin cire tallafin ba su yi amanna ko gaskata gwamnati cewa idan ta cire ɗin za ta aikata abin alheri da kuɗin ba.
Akwai da yawa waɗanda su ka ƙi yarda da batu cire tallafin fetur a 2012, saboda siyasar da ke tattare da lamarin ko kuma siyasar da ta yi katutu a zuciyar su.
Ko ma dai wane matsayi mutum zai ɗauka dangane da goyon baya ko rashin goyon bayan cire tallafin fetur, to ni dai a tsawon shekaru na ga mutane da yawa idan tafiya ta yi tafiya su na canja matsayin da su ka ɗauka da farko.
Abin lura kuma abin da ya ƙara fitowa fili daga Janairu 2012 zuwa Yuni 2023, ya nuna cewa dangantakar da ke tsakanin gwamanti da ‘yan ƙasa ba mai ƙarko ba ce. Hakan kuwa ya sa jama’a ba su yi wa gwamnati kallon ƙima ko kallon mai gaskiya da riƙon amanar jama’a, musamman idan wani tsari na ƙasa ya taso.
Cikin 2012, rahoton Cibiyar Brookings da ke birnin Washington DC, ya bayyana cewa a cikin shekarar 2012, Najeriya ta biya Naira biliyan 8 kuɗin tallafin fetur.
Da ya ke a lokacin akwai ‘yan ƙarambosuwa a harkar cire tallafin fetur, an yi ittifaƙin adadin kuɗin ba daidai su ke ba, ko dai an noƙe wasu, ko kuma an yi zulaƙen maƙudan kuɗaɗe da yawa an karkatar da su. Saboda hukumomin gwamnati daban-daban a lokacin kowa na faɗin adadin kuɗaɗen biyan tallafin da ya ce su ke daidai.
Misali, lokacin da hayaƙin zanga-zangar tallafin fetur ya tashi a Janairu, 2021, CBN cewa ya yi Najeriya ta biya naira tiriliyan 1.7 na tallafin fetur a 2011.
To ko abin da aka ce an kashe a 2012, shi ma an riƙa yin jayayyar haƙiƙanin adadin.
Ƙarin abin damuwar kuwa shi ne daga wancan lokacin zuwa yanzu, kuɗaɗen tallafin da ake cirewa duk shekara sun ƙaru sosai, fiye da hankalin mai hankali, kuma fiye da tunanin mai tunani.
Wata jarida ma a kwanan nan ta ce a cikin shekaru 18 Najeriya ta biya kuɗin tallafin fetur har Naira Tiriliyan 21.7, bisa da la’akari ko kafa hujja da ƙididdigar NEITI.
Misali, a cikin kasafin 2023, Gwamnatin Najeriya ta ware naira tiriliyan 3.36 domin biyan kuɗin tallafin fetur tsawon watanni shida. Wato kenan duk wata za a biya Naira biliyan 540.
Amma kuma a farkon shekarar 2022, Gwamnatin Tarayya ta yi kasafin kashe Naira tiriliyan 4 kan tallafin fetur. Abin haushi da takaici, amma Naira biliyan 826.9 kacal aka ware wa ɓangaren kiwon lafiya a waccan shekara.
Ana kukan targaɗe kuma sai ga karaya. Yayin da ake cikin damuwar ɗimbin bashin da ke wuyan Najeriya, tare da samun wawakeken giɓin kasafin kuɗi, maganar gaskiya dai ko an ƙi, ko an so tallafin fetur babbar barazana ce da ka iya durƙusar da Najeriya.
Cikin 2022 dai Najeriya ta kashe kashi 96.3 na kuɗaɗen shigar da ta tara a shekarar wajen biyan basussuka. A shekarar 2021 kuwa kashi 83.2 ta kashe na kuɗaɗen shigar ƙasar, duk su ka tafi a biyan basussuka.
A yau kuma tallafin fetur ɗin ya ma fi yi wa ƙasar nan barazana, saboda a yanzu da wahala gwamnati ta ke biyan kuɗaɗen tallafin.
Tallafin Fetur: An Ƙi Cin Biri An Ci Kare:
CIkin shekarar 2022 sai da gwamnatin tarayya ta ciwo bashin Dalar Amurka biliyan 1.25 da Euro kuma kashe 8.375 sannan ta iya biyan kuɗaɗen tallafin fetur. Wannan bayani fa ya fito ne daga bakin tsohuwar Ministar Harkokin Kuɗaɗe, Zainab Ahmed.
Zainab ta shaida wa Reuters haka, lokacin da ake tattauna karɓo bashin Euro biliyan 2.2.
Dama a cikin 2022 Shugaban NNPCL, Mele Kyari ya ce Najeriya ta kakare, ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗaɗen tallafin mai ba.
Kyari ya ƙara da cewa a yanzu haka NNPC ta na bin Gwamantin Tarayya bashin Naira tiriliyan 2.8 ba tallafin fetur ɗin da ba ta kai ga biya ba tukunna.
Wato dai kawai kowa ya kamata ya fahimci cewa babu wasu kuɗaɗe da za a iya adanawa idan ma an daina biyan kuɗaɗen tallafin. Saboda basussuka kawai za a riƙa biya.
Cire Takalmin Fetur: Barbaɗa Wa Mai Ciwon Ido Barkono Da Sunan Magani:
Ciwon da talaka zai fi ji a jikin sa, shi ne yadda aka cire masa tallafin fetur, daidai lokacin da malejin tsadar rayuwa a cilla sama da kashi 22.2%, sannan kuma yawan majiya ƙarfi marasa aikin yi ya ƙaru sosai zuwa kashi 24 bi sa 100. Ga yunwa, ta fatara da talauci. Ba wutar lantarki gangariya.
Tsadar sufuri ya nunka saboda nunkawar farashin litar fetur.
Kalubalen Gwamnatin Tarayya a fili ya ke. Na farko dai an yi sakaci gwamnatocin baya sun kasa soke tallafin fetur tun daga 2012 har zuwa Mayu 2023.
Sauƙin abin dukkan ‘yan takara uku, Tinubu, Obi da Atiku duk sun bayyana cire tallafi idan sun hau mulki.
Ko ma dai me kenan, azarɓaɓin da Tinubu ya yi tun kafin ya zauna kan kujerar mulki da ya ce, “tallafin fetur ya wuce faufaufau”, ya zo a cikin gaggawa, domin ya shammaci kowa ba cikin shiri ba.
Discussion about this post