An ɗage ganawar da Shugaba Bola Tinubu zai yi da Wakilan Majalisa na ɓangaren adawa zuwa ranar Alhamis.
Tun da farko dai an tsaya taron ganawar a ranar Litinin, ƙarfe 3 na yamma da kuma ƙarfe 5 na yamma, a Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja.
Sai dai kuma PREMIUM TIMES ta ji cewa an ɗage ganawar zuwa ranar Alhamis, ba tare da bayyana dalili ba.
Zaɓaɓɓen Ɗan Majalisar Tarayya Ikenga Ugochinyere daga Imo, ya tabbatar da labarin ɗage taron a wata tattaunawa da aka yi da shi.
Maimakon ganawa da su, Tinubu ya gana da tsohon Gwamnan Ribas, Nyesom Wike, tsohon Gwamnan Ebonyi kuma Zaɓaɓɓen Sanata, David Umahi da Godswill Akpabio, Sanatan da ke neman Shugabancin Majalisar Dattawa.
Tinubu ya na goyon bayan Akpabio, tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom shi da Barau Jibrin, Sanatan Kano.
A Majalisar Tarayya kuma Tinubu na goyon bayan Tajuddeen Abbas daga Jihar Kaduna, shi da Ben Kalu daga Jihar Abiya.
Sai dai kuma waɗanda Tinubu ke goyon baya a Majalisar Dattawa da ta Tarayya, duk su na fuskantar tirjiya daga masu neman muƙaman daban-daban.
A Majalisar Tarayya cikin waɗanda ke neman zama Kakakin Majalisa akwai Tajuddeen Abbas, zaɓin Tinubu da APC, Muktar Betara, Yusuf Gagdi, Sada Soli, Aminu Jaji, sai kuma Miriam Onuoha.
Tinubu na so ya gana da zaɓaɓɓun sanatocin da mambobin tarayya ɗin ne kafin ranar 13 Ga Yuni, ranar da za a rantsar da su.
Taron na da nasaba da ƙoƙari da buƙatar Tinubu ya ga cewa Akpabio da Jibrin sun yi nasara, kamar yadda hakan ya ke so ya ga Abbas da Kalu sun yi nasara.
A ciki sanatoci 109, APC na da 59, sauran jam’iyyu shida kuma, PDP na da 36, LP 8, SDP 2, NNPP 2, YPP 1 sai APGA 1, su shida masu adawa na da Sanatoci 50 kenan.
Cukumurɗar ta fi zafi a Majalisar Wakilai ta Ƙasa, inda wakilan tarayya su 360 ne, amma gungun wakilan ‘yan adawa sun fi yawan wakilan APC.
APC na da wakilai 178, PDP 114, LP 35, NNPP 19, APGA 5, ADC 2, SDP 2 sai YPP 1.
Jam’iyyun adawa na da wakilai 182 cif-da-cif kenan.
Discussion about this post