Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu, Kashim Shettima, Sakataren Gwamnati da Gwamnonin Najeriya ne su ka yi masa taron-dangin kayar da shi, ba ƙaramin ƙwaro Godswill Akpabio ba.
Yari wanda ke wakiltar Zamfara ta Yamma, ya bayyana haka ne a hirar sa da BBC Hausa, ranar Juma’a.
A lokacin zaɓen dai Sanata Godswill Akpabio ya samu ƙuri’u 63, shi kuma Yari 46 a cikin Sanatoci 109.
Akpabio dai shi Tinubu, APC da gwamnoni ke so ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Yari ya ce ai ba don Tinubu ya yi masa taron dangi ba, to shi ne zai yi nasara, ba Akpabio ba.
Ya ce ai ya na da yaƙinin cewa zai yi nasara, shi ya sa har ya shiga takarar.
“Idan na san ba zan yi nasara ba, to ba ma zan fara shiga takarar ba. Don haka ba don Tinubu ya yi min taron da dangi ba, to da ni zan yi nasara.”
“Ban yi tunanin faɗuwa zaɓe ba ko a mafarki. Saboda daga ranar da muka fara lissafa waɗanda ke tare da mu, sai na gane cewa ina da mafiya rinjaye. To amma ka sani ba da Akpabio kaɗai na yi takara ba. Taron dangi aka yi mani.” Cewar Yari.
Ya ce waɗanda ya yi takarar da su, har da Shugaba Bola Tinubu, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Sakataren Gwamnati da Gwamnoni da sauran manyan jiga-jigan siyasa da gwamnati.
“Ina fatan a zango mai zuwa na 2027, Tinubu zai ƙyale dimokuraɗiyya ta yi aikin ta.”
Discussion about this post