Sabuwar Majalisar Dattawa ta 10 ta zaɓi Sanata Godswill Akpabio daga jihar Akwa Ibom sabon Shugaban Majalisar Dattawa.
Sanata Barau Jibrin daga Jihar Kano aka zaɓa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.
Akpabio ya fito daga Kudu maso Gabas, shi kuma Barau Jibrin daga Arewa maso Yamma.
Akpabio ya kayar da Sanata Abdul’aziz Yari daga Jihar Zamfara, inda ya samu ƙuri’u 63, shi kuma Yari 46.
an fara zaɓe tun ƙarfe 8:45 na safe, a Zauren Majalisar Dattawa, wanda nan da nan aka rantsar da Akpabio bayan an zaɓe shi.
Akpabio shi ne Shugaban Majalisar Dattawa na 9, bayan dawowar dimokraɗiyya wato a Jamhuriya ta Huɗu.
Sanata Barau Jibrin ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ba tare da samun mai hamayya ba.
Sanata David Umahi da Sanata Sani Mustapha na Jihar Kwara ne su ka nemi a zaɓe shi, kuma aka amince.
Akpabio tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ne, wanda bayan saukar sa cikin 2015 a ƙarshen mulkin Goodluck Jonathan, aka zarge shi da wawure Naira biliyan 102.
Discussion about this post