Ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ci gaba da damƙa wa kotu bayanan hujjojin da ya ke bayarwa domin kotu ta ƙwace nasarar da INEC ta ce Bola Tinubu na APC ya yi ta ba shi, ko kuma a sake zaɓe ɗungurugum.
A ranar Talata ce Obi ya gabatar wa kotu rahotannin da INEC ta fitar dangane da Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe (IReV), a Abuja.
INEC dai tun kafin zaɓe ta yi alƙawarin cewa za ta watsa sakamakon zaɓe daga BVAS zuwa Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe (INEC) yadda kowa zai shiga manhajar, wato ‘portal’ don ya ga kwafe-kwafen sakamakon zaɓen kowace rumfar zaɓe, bayan kammala zaɓe. Amma ba ta yi hakan ba.
Wannan rashin cika alƙawarin da INEC ta yi ya harzuƙa dama a ƙasar nan da masu sa-ido.
Hakan na daga cikin manyan dalilan da su ka sa Peter Obi ya garzaya kotu, ya yi zargin an yi maguɗi a zaɓen.
Obi ya yi zargin INEC ta haɗa baki da Tinubu an yi masa maguɗi.
A ci gaba da sauraren ƙara a ranar Talata, lauyan Obi mai suna Peter Afoba, wanda Babban Lauya ne, ya gabatar wa kotu rahoton Manhajar IReV daga jihohi biyar da su ka haɗa da Ribas, Akwa Ibom, Ekiti, Ogun da kuma Adamawa.
Ya shaida wa kotu cewa dukkan rahotannin sai da INEC ta tabbatar da cewa ita ce ta fitar da shi.
Afoba ya shaida wa kotu cewa rahotannin akwai wasu daga ƙananan hukumomi 21 na Adamawa, 20 daga Ogun, 16 daga Ekiti, 19 daga Ribas da kuma 25 daga Akwa Ibom.
Saɓanin yadda INEC ta bayyana, wani nazari da PREMIUM TIMES ta yi ya nuna cewa LP ce ta lashe zaɓe a Jihar Ribas, ba Tinubu ba, kamar yadda INEC ta bayyana.
Sai dai lauyan INEC Kemi Pinheiro shi da lauyan APC da na TInubu duk sun ƙi yarda a gabatar da kwafen bayanan. Amma duk da haka kotu ta karɓa.
Wani lauyan Obi mai suna Audu Onuga, ya ƙara maka wa kotu kwafe-kwafen bayanan ƙoƙarin ganin an haramta wa Tinubu wasiƙa zaɓen 2023.
Ɗan takarar shugaban ƙana na LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ƙara danƙara wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa wasu kwafe-kwafen bayanan da ya ce ke da alaƙa da rashin sahihancin zaɓen shugaban ƙasa, wanda INEC ta shirya a ranar 25 ga Maris, 2023.
Kwafen takardun bayanan dai duk sun ƙunshi sakamakon zaɓuɓɓuka da kuma rahotannin da INEC ta yi dangane da yadda aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
Obi ya maka APC, Bola Tinubu, Kashim Shettima da INEC a kotu, inda ya ke ƙalubalantar nasarar da INEC ta ce Tinubu na APC ya yi.
Bayanan da Peter Obi ya maka wa kotu a ranar Talata, ta hannun lauyan sa kuma (SAN), Peter Afoba, sun haɗa da fam-fam masu lamba EC40GPU, EC40G1 da kuma rahotannin da INEC ta riƙa bayarwa bayan kammala zaɓen.
Peter Obi ya maka wa kotu fam mai lamba EC40GPU har guda 45 daga ƙananan hukumomi 10 na Jihar Neja, sai wasu 23 daga ƙananan hukumomi bakwai na Jihar Osun.
Sannan akwai wasu 17 daga ƙananan hukumomi uku na jihar Edo, sai kuma fam 52 daga ƙananan hukumomi biyar na Jihar Sokoto.
Peter Obi har ila yau ya maka wa kotu fam-fam mai lamba EC40G guda 15 daga ƙananan hukumomi takwas na Jihar Osun, sai wasu fam-fam masu lamba EC40G1 daga ƙananan hukimomi 12 na jihar Edo.
Akwai kuma fam-fam 15 masu lamba EC40G daga ƙananan hukumomi huɗu na jihar Sokoto, sai wasu tara daga ƙananan hukumomi biyu na Jihar Sokoto, masu lamba EC40G1.
Peter Obi ya kuma bai wa kotu kwafen rahotannin da INEC ta yi dangane da yadda zaɓen shugaban ƙasa ya kaya a Neja, Edo, tare da zargin an tafka maguɗi lokacin gudanar da zaɓen.
Ya kuma maka wa kotu rahoton INEC kan Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (IRev) na ƙananan hukumomi 21 daga jihar Adanawa, wasu kuma daga Ogun, wasu daga Ekiti, Ribas da Akwai Ibom.
Fam EC40G: Fam ne mai ɗauke da bayanan adadin ƙuri’un wuraren da ba a yi zaɓe ba, ko aka soke zaɓen.
Fam EC40GPU: Mai ɗauke da bayanan lokacin da aka yi zaɓe a rumfar zaɓe.
Sai dai lauyoyin Tinubu, INEC da na APC da Kashim Shettima duk nuna wa kotu cewa ba su goyi bayan Obi ya gabatar da kwafe-kwafen bayanan a kotu ba.
Kotun dai a ƙarƙashin jagorancin sauran alƙalai huɗu, Haruna Tsammani ya ɗage zaman ta zuwa washegari Laraba.
Discussion about this post