Ɗan takarar shugaban ƙana na LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ƙara danƙara wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa wasu kwafe-kwafen bayanan da ya ce ke da alaƙa da rashin sahihancin zaɓen shugaban ƙasa, wanda INEC ta shirya a ranar 25 ga Maris, 2023.
Kwafen takardun bayanan dai duk sun ƙunshi sakamakon zaɓuɓɓuka da kuma rahotannin da INEC ta yi dangane da yadda aka gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.
Obi ya maka APC, Bola Tinubu, Kashim Shettima da INEC a kotu, inda ya ke ƙalubalantar nasarar da INEC ta ce Tinubu na APC ya yi.
Bayanan da Peter Obi ya maka wa kotu a ranar Talata, ta hannun lauyan sa kuma (SAN), Peter Afoba, sun haɗa da fam-fam masu lamba EC40GPU, EC40G1 da kuma rahotannin da INEC ta riƙa bayarwa bayan kammala zaɓen.
Peter Obi ya maka wa kotu fam mai lamba EC40GPU har guda 45 daga ƙananan hukumomi 10 na Jihar Neja, sai wasu 23 daga ƙananan hukumomi bakwai na Jihar Osun.
Sannan akwai wasu 17 daga ƙananan hukumomi uku na jihar Edo, sai kuma fam 52 daga ƙananan hukumomi biyar na Jihar Sokoto.
Peter Obi har ila yau ya maka wa kotu fam-fam mai lamba EC40G guda 15 daga ƙananan hukumomi takwas na Jihar Osun, sai wasu fam-fam masu lamba EC40G1 daga ƙananan hukimomi 12 na jihar Edo.
Akwai kuma fam-fam 15 masu lamba EC40G daga ƙananan hukumomi huɗu na jihar Sokoto, sai wasu tara daga ƙananan hukumomi biyu na Jihar Sokoto, masu lamba EC40G1.
Peter Obi ya kuma bai wa kotu kwafen rahotannin da INEC ta yi dangane da yadda zaɓen shugaban ƙasa ya kaya a Neja, Edo, tare da zargin an tafka maguɗi lokacin gudanar da zaɓen.
Ya kuma maka wa kotu rahoton INEC kan Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (IRev) na ƙananan hukumomi 21 daga jihar Adanawa, wasu kuma daga Ogun, wasu daga Ekiti, Ribas da Akwai Ibom.
Fam EC40G: Fam ne mai ɗauke da bayanan adadin ƙuri’un wuraren da ba a yi zaɓe ba, ko aka soke zaɓen.
Fam EC40GPU: Mai ɗauke da bayanan lokacin da aka yi zaɓe a rumfar zaɓe.
Sai dai lauyoyin Tinubu, INEC da na APC da Kashim Shettima duk nuna wa kotu cewa ba su goyi bayan Obi ya gabatar da kwafe-kwafen bayanan a kotu ba.
Kotun dai a ƙarƙashin jagorancin sauran alƙalai huɗu, Haruna Tsammani ya ɗage zaman ta zuwa washegari Laraba.
Discussion about this post