Ƙoƙarin da ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ya yi domin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ba shi iznin yi wa jami’an Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wasu tambayoyin ‘yar-ƙure, ya ci tura, domin ita INEC ɗin ta nuna ƙin amincewa a bai wa Obi wannan iznin da ya nema.
Ba INEC kaɗai ce ta nuna rashin amincewa ba, shi ma wanda ake ƙara na farko, wato Bola Tinubu da kuma APC duk sun nuna ƙin amincewar su a ranar Alhamis.
Obi ya nemi kotun ta ba shi iznin yi wa wasu jami’an ICT na INEC wasu tambayoyin ƙwaƙwaf.
Ya ce lauyoyin sa ne za su yi wa jami’an INEC waɗanda da su aka yi aikin zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Ya na so a yi masu tambayoyin ne dangane da amfani da intanet a ranar da aka yi zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu.
Peter Obi ya yi zargin cewa INEC ta yi masa ƙwangen ƙuri’u, a ɗaya gefen kuma ta yi wa Tinubu na APC aringizo.
Duk a ranar Alhamis ɗin ce dai Atiku Abubakar na PDP ya gabatar da jami’an INEC biyu su ka bayar da shaida a gaban kotu.
Marƙabu Da Ja-in-ja A Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa:
Yayin da aka kai ga batun ƙarar da Obi ya shigar a zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan sa Patrick Ikweto ya nemi sanin ainihin gejin ƙwarewar jami’an INEC na ICT, waɗanda su ka yi aikin zaɓen shugaban ƙasa.
Ikweto ya roƙi kotu ta umarci INEC ta ba shi sunayen jami’an ICT na INEC da ta ce ƙwararru ne, waɗanda su ka sarrafa na’urorin INEC a ranar zaɓe.
Gungun lauyoyin Obi sun shaidawa kotu cewa idan har INEC ta ba su sunayen da su ka nemi a ba su, to hakan zai taimaka su san irin tambayoyin da za su yi musu.
INEC, TINUBU Da APC Sun Nuna Rashin Amincewa:
Lauyan INEC, Kemi Pinheiro wanda Babban Lauya ne (SAN), ya nuna rashin amincewa da roƙon da Obi ya yi domin kotu ta ba shi iznin yi wa Jami’an INEC tambayoyi. Ya ce roƙon na Obi bai ma cancanta ba.
Ya ce tun kafin a fara sauraren ƙara ya kamata a ce Obi ya nemi wannan izini daga kotu, ba yanzu ba.
“Tunda kotu ta shafe makonni biyu ta na zaman share-fagen fara sauraren ƙararrakin zaɓe, kuma a lokacin aka ƙayyade irin yadda za a riƙa gabatar da ba’asin ƙararraki.
“Don haka a yanzu dai kotu ba ta da hurumin bai wa Obi wannan iznin da ya nema daga baya.” Inji Lauyan INEC.
Shi ma lauyan Tinubu Akin Olujimi da Lateef Fagbemi na APC duk ba su amince a bai wa Peter Obi yi wa jami’an INEC tambayoyi a gaban kotu ba.
A yau Juma’a ne kotun za ta yanke hukuncin bai wa Obi iznin da ya nema, ko kuma ta hana shi.
Discussion about this post