Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta zare wa lauyoyin ɗan takarar LP, Peter Obi idanu, saboda ɓata lokaci da jan-ƙafa a sauraren ƙararrakin zaɓe.
Lamarin ya faru kwana ɗaya bayan kotun ta gargaɗi lauyoyin dangane da sakamakon da ka iya faruwa bayan sun nemi a ɗage sauraren ƙara a ranar Alhamis.
To a ranar Alhamis ɗin ce kotu ta nuna wa lauyoyin LP da na Peter Obi ɓacin rai, saboda ɓata lokacin da su ka ƙirƙiro a zaman sauraren ƙararrakin rashin amincewa da nasarar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya samu a zaɓen 25 ga Fabrairu.
Alƙalan kotun su biyar a ƙarƙashin Babban Mai Shari’a Haruna Tsammani, sun nuna masu ɓacin rai saboda lauyoyin su kasa tsara matakan da ya dace su riƙa gabatar da shaidu a kotun.
Hakan ya faru kuma kwana ɗaya bayan lauyoyin Peter Obi sun nemi a ɗage ƙara, saboda ɗaya daga cikin lauyoyin ba shi da lafiya bai halarci kotun ba.
Yayin da aka koma ci gaba da sauraren ƙarar a ranar Alhamis, sai kotu ta nuna wa lauyoyin ɓacin rai matuƙa, saboda lauyoyin sun kasa gabatar da tsari da matakan bijiro wa kotu hujjoji da shaidu.
Hakan ya kai ga kotu dakatawar wasu ‘yan mintina, domin a bai wa lauyoyin a ƙarƙashin Awa Kalu damar kimtsa tsarin shigar da hujjoji da shaidun da hujjojin a kotu.
Bayan an koma sauraren ƙara, har yau dai kotun ta ƙara cewa kwafe-kwafen da lauyoyin su ka sake gabatarwa ba a daidai su ke ba. Kuma ba su cika sharuɗɗan da kotu ta gindaya ba.
Lamarin dai sai da ya kai alƙalan kotun sun umarci lauyoyin LP da na Peter Obi cewa za a sake ɗage sauraren ƙarar, domin a ba su damar sake zuwa su zauna su tsara matakan shigar da shaidu da hujjoji kamar yadda kotu ta tsara.
Ɗaya daga cikin mambobin alƙalan kotun, Misitura Bolaji-Yusuf, ƙarara ya shaida wa lauyoyin cewa abin da su ke yi ɓata lokacin kotu ne fa.
“To yau dai ba mu yi komai ba. Kun jawo mana ɓata lokaci kawai. Saboda irin yadda ku ka gabatar da kwafen bayanan hujjojin ku, tsari ne na ‘yan dagaji. Hakan kuma zai iya jawo wa ku kan ku da kuma kotu afkawa cikin ruɗani.”
Discussion about this post