Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yi fatali da roƙon da ɗan takarar jam’iyyar LP, Peter Obi ya yi, inda ya nemi iznin a ba shi dama ya gayyaci wasu jami’an kula da na’urorin zaɓe na INEC, domin ya yi masu tambayoyin ƙwaƙwaf.
Obi ya ce shi kan sa a matsayin sa na ɗan takara da kuma jam’iyyar sa LP ke ƙalubalanatar sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Ya yi zargin cewa INEC ta yi masa ƙwangen ƙuri’u, sannan ta yi wa Bola Tinubu na APC aringizo, kuma ta ayyana cewa shi ya ci zaɓe.
Sai dai lauyan INEC da na APC duk sun ƙi amincewa Peter Obi ya yi wa jami’an tambayoyi, a ranar 8 ga Yuni, lokacin da ya shigar da buƙatar a yayin sauraren ƙarar.
Hukuncin Kotu:
A ranar Asabar 10 ga Yuni, alƙalan kotun su biyar a ƙarƙashin jagorancin Babban Mai Shari’a Haruna Tsammani, sun ce lauyoyin Peter Obi sun yi kuskure, domin ba su shigar da buƙatar ta su a lokacin da Dokar Zaɓe ta 2022 ta ƙayyade ba.
Kotun cewa ta yi, “Duk jam’iyya ko mai ɗan takarar da ya shigar da ƙarar zaɓe, idan ya na so ya ƙara kinkimo wasu batutuwa a cikin ƙarar, to zai iya yi, amma kada ya wuce kwanaki 10 bayan wanda ake ƙara ya maido amsar karɓar sammacin ƙarar sa da aka shigar.
“Idan kuwa bai maida amsa a lokacin ba, to kotu za ta iya hana shi neman yin hakan,” haka Haruna Tsammani ya karanto daga cikin Kundin Dokar Zaɓe na 2022, a lokacin da su ke yin fatali da roƙon da Peter Obi ya yi.
Obi da LP sun shigar da bayanan ƙara a ranar 21 ga Afrilu, yayin da ya nemi yi iznin yi wa jami’an ICT na INEC tambayoyi a ranar 23 ga Mayu.
A kan haka ne INEC ta ce ranakun da Dokar Zaɓe ta 2022 ta ƙayyade sun wuce.
“Don haka kotu ba za ta ɗaga wa mai ƙara ƙafar yi masa ƙarin kwanakin da Dokar Zaɓe ta haramta a yi ba.
Idan Za A Tuna;
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa Peter Obi na so kotu ta ba shi iznin yi wa wasu jami’an ICT na INEC tambayoyi masu sarƙaƙiya, INEC, APC da Tinubu sun ƙi yarda.
Ƙoƙarin da ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na LP, Peter Obi ya yi domin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta ba shi iznin yi wa jami’an Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wasu tambayoyin ‘yar-ƙure, ya ci tura, domin ita INEC ɗin ta nuna ƙin amincewa a bai wa Obi wannan iznin da ya nema.
Ba INEC kaɗai ce ta nuna rashin amincewa ba, shi ma wanda ake ƙara na farko, wato Bola Tinubu da kuma APC duk sun nuna ƙin amincewar su a ranar Alhamis.
Obi ya nemi kotun ta ba shi iznin yi wa wasu jami’an ICT na INEC wasu tambayoyin ƙwaƙwaf.
Ya ce lauyoyin sa ne za su yi wa jami’an INEC waɗanda da su aka yi aikin zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Ya na so a yi masu tambayoyin ne dangane da amfani da intanet a ranar da aka yi zaɓen shugaban ƙasa a ranar 25 ga Fabrairu.
Peter Obi ya yi zargin cewa INEC ta yi masa ƙwangen ƙuri’u, a ɗaya gefen kuma ta yi wa Tinubu na APC aringizo.
Duk a ranar Alhamis ɗin ce dai Atiku Abubakar na PDP ya gabatar da jami’an INEC biyu su ka bayar da shaida a gaban kotu.
Marƙabu Da Ja-in-ja A Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓen Shugaban Ƙasa:
Yayin da aka kai ga batun ƙarar da Obi ya shigar a zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan sa Patrick Ikweto ya nemi sanin ainihin gejin ƙwarewar jami’an INEC na ICT, waɗanda su ka yi aikin zaɓen shugaban ƙasa.
Ikweto ya roƙi kotu ta umarci INEC ta ba shi sunayen jami’an ICT na INEC da ta ce ƙwararru ne, waɗanda su ka sarrafa na’urorin INEC a ranar zaɓe.
Gungun lauyoyin Obi sun shaidawa kotu cewa idan har INEC ta ba su sunayen da su ka nemi a ba su, to hakan zai taimaka su san irin tambayoyin da za su yi musu.
INEC, TINUBU Da APC Sun Nuna Rashin Amincewa:
Lauyan INEC, Kemi Pinheiro wanda Babban Lauya ne (SAN), ya nuna rashin amincewa da roƙon da Obi ya yi domin kotu ta ba shi iznin yi wa Jami’an INEC tambayoyi. Ya ce roƙon na Obi bai ma cancanta ba.
Ya ce tun kafin a fara sauraren ƙara ya kamata a ce Obi ya nemi wannan izini daga kotu, ba yanzu ba.
“Tunda kotu ta shafe makonni biyu ta na zaman share-fagen fara sauraren ƙararrakin zaɓe, kuma a lokacin aka ƙayyade irin yadda za a riƙa gabatar da ba’asin ƙararraki.
“Don haka a yanzu dai kotu ba ta da hurumin bai wa Obi wannan iznin da ya nema daga baya.” Inji Lauyan INEC.
Shi ma lauyan Tinubu Akin Olujimi da Lateef Fagbemi na APC duk ba su amince a bai wa Peter Obi yi wa jami’an INEC tambayoyi a gaban kotu ba.
A yau Juma’a ne kotun za ta yanke hukuncin bai wa Obi iznin da ya nema, ko kuma ta hana shi.
Discussion about this post