Ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, ya yi zargin cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta hana shi kai hannu kan bayanan na’urar zaɓe, waɗanda ya ce da su ne zai yi amfani ya nuna wa kotu da kuma duniya shaidar cewa an yi masa maguɗi a zaɓen, wanda ya gunada a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Atiku na iƙirarin shi ne ya ci zaɓe, amma aka murɗe, aka bai wa Bola Tinubu na APC.
Atiku ya ce duk da cewa ya biya kuɗin ba shi bayanan har Naira miliyan 6, amma sai sa-toka-sa-katsi ya ke yi tsakanin sa da INEC, ta hana shi bayanan.
A ranar Talata ɗin nan ce aka ci gaba da zaman kotu, a Abuja, inda lauyan Atiku,Eyitayo Jegede ya shaida wa kotu cewa ya na samun cikas sosai daga ɓangaren INEC, saboda hukumar ta ƙi bai wa gungun lauyoyin sa bayanan na’urar zaɓe, domin su kafa hujjar an yi maguɗi da su.
Jegede wanda babban lauya ne (SAN), ya na so ya gabatar wa kotu sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 10 daga cikin 21 na jihar Kogi, domin ya kafa hujja da kaɗan daga maguɗin zaɓen da aka yi.
Atiku na so ya gabatar da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Ankpa, Dekina, Idah, Ofu, Olamoboro, Yagba ta Gabas, Yagba ta Yamma, Kabba Nunu da kuma Igalamela Odolu.
Yayin da Jegede ya nemi gabatar da waɗannan bayanai, Alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin Haruna Tsammani, sun ce masa ba daidai ba ne ya riƙa gabatar da su da kaɗan kaɗan, sai dai ya gabatar da su baki ɗaya.
A nan ne Jegede ya shaida wa kotu cewa ya nemi INEC ta ba shi kwafen bayanan, shi da sauran lauyoyin da ke ƙarƙashin sa, amma INEC ta ƙi ba sh.
Ya shaida wa kotu cewa har Naira miliyan 6 da aka caji Atiku kafin a fito masa da bayanan zaɓen, duk Atiku ya biya, amma har zuwa yau ɗin nan, INEC ta hana.
Daga nan Jegede ya nemi a ɗage shari’ar zuwa kwana ɗaya kacal, domin ya sake rubuta INEC wata wasiƙar nan ba ba shi kwafen sakamakon zaɓen.
Lauyan INEC dai bai ce komai ba, bai magana kan ɗage sauraren ƙarar da kwana ɗaya ba.
Discussion about this post