Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu zai bayyana a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a ranar Alhamis, a Abuja.
Yakubu zai bayar da shaida a kan ƙarar da ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya maka Bola Tinubu, INEC da APC, inda ya nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, wanda Tinubu ya yi nasara.
Lauyan Atiku, Chris Uche ne ya bayyana wa alƙalan kotun su biyar bisa jagorancin Haruna Tsammani cewa Yakubu zai bayyana a kotun ranar Alhamis.
Lauyoyin Atiku ne su ka gayyaci Yakubu tare da aika masa sammacin bayyana domin ya amsa tambayoyin da za su yi masa dangane da jayayyar da Atiku ke yi kan sakamakon zaɓen.
Atiku shi ne ya zo na biyu, yayin da Peter Obi na LP ya zo na uku.
Sannan kuma lauyoyin su ka son Yakubu ya damƙa wa kotun wasu muhimman bayanan zaɓen shugaban ƙasa.
Babban Lauya Chris Uche, ya sanar da lauyoyin INEC da na APC cewa Yakubu zai bayyana a ranar Alhamis. Ya ce ya sanar da su ne don kada a kawo wani abin da zai haifar da cikas ga sauraren ƙara a ranar.
Zuwa yanzu dai Atiku ya kira masu bayar da shaida har mutum 18. Amma a ranar Talata, lauyan Atiku ya kira mai bayar da shaida na ranar da suna “Babban Mai Bada Shaida”.
Mai bayar da shaidar wato Alex Ter, lauya ne kuma tsohon Antoni Janar, tsohon Kwamishinan Shari’a na Jihar Benuwai.
Da ya ke bayani a gaban kotu, Alex Ter ya yi zargin cewa an yi gagarimin aikata rashin daidai a zaɓen shugaban ƙasa da INEC ta shirya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Ya ƙara da cewa zaɓen cike ya ke da kauce wa Dokar Zaɓe ta 2022.
A bayanin da ya yi bayan ya yi rantsuwa, Ter ya ce shi ne Kodinatan Dakin Lura da Zaɓe na PDP Situation Room) a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, a Abuja.
Daga nan ya gabatar wa kotu da bidiyo-bidiyo da aka nuno Shugaban INEC Yakubu da Kwamishinan Wayar da Kai na INEC, Festus Okoye, su biyun su na ƙara jaddada cewa INEC za ta tura sakamakon zaɓe daga na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) zuwa Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe, wato iRev.
Kwafen bidiyo na uku da ya gabatar ya ƙunshi Shugaban Sa-ido na Kungiyar Tarayyar Turai, wanda kotun ta karɓa shi ma a matsayin shaida.
Sannan Kotun Zaɓe ta karɓi kwafen ƙa’idojin aikace-aikacen da su ka wajaba a kan jami’an zaɓe na 2022 da na 2023, a matsayin shaida duk daga hannun Alex Ter.
Ba a nan lauya Ter ya tsaya ba, ya kuma damƙa wa kotu hoton shafin Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe (IReV) na INEC.
Duk da lauyoyin INEC da na Atiku sun nuna rashin amincewar su, kotun ta karɓi dukkan kwafe-kwafen bidiyon da Alex Ter ya kunna aka kalla a kotun, a matsayin shaida daga ɓangaren Atiku.
A yau Laraba za a ci gaba da kafsawa.
Discussion about this post