A ranar Juma’a ce Atiku Abubakar da Peter Obi su ka kammala gabatar wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa shaidu da kuma tulin hujjojin su.
Yayin da Atiku ya gabatar da masu shaida 27, Peter Obi ya gabatar da 13.
Haka a ranar Juma’a ɗin Atiku ya gabatar da kwafen bayanan Jami’ar Jihar Chicago.
Farkon mako ne mai bada shaidar Atiku ya ce wa kotu INEC ta goge sakamakon zaɓen da ke cikin na’urar BVAS.
Wani majalisa bada shaida a shari’ar zaɓen shugaban ƙasa, wanda Atiku da PDP su ka gabatar, ya shaida wa alƙalan kotun cewa INEC ta goge dukkan sakamakon zaɓen da ke cikin Na’urar Tantance Masu Shaidar Rajistar Katin Zaɓe, wato BVAS.
Wannan na’urar dai INEC ta rattaba su a dukkan rumfunan zaɓe sama da 176,000 a faɗin ƙasar nan, lokacin zaɓen 2023.
Mai bayar da shaida Hitler Nwala, wanda ƙwararren masanin sarrafa na’urorin zamani ne, ya shaida wa kotu cewa ya bibiyi BVAS 110 da aka yi zaɓe da su a FCT Abuja, amma ya samu duk INEC ta goge sakamakon zaɓen da ke cikin su, kafin hukumar zaɓen ta bayar a bibiye su.
Lauyan Atiku Abubakar, wato Chris Uche ne ya gabatar da mai bada shaidar.
A makon jiya kuma an gabatar da Dino Melaye a matsayin mai bada shaida, inda shi ma ya rantse a kotu cewa an yi ƙwange da aringizon sakamakon zaɓe don a kayar da Atiku.
Kakakin Yaɗa Labaran Kamfen ɗin Atiku Abubakar, Dino Melaye, ya bayyana gaban Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, a matsayin mai bayar da shaida na Atiku Abubakar.
Melaye wanda ya bayyana a matsayin mai bayar da shaida na musamman ga Atiku Abubakar, ya bayyana cewa sakamakon ƙarshe na zaɓen shugaban ƙasa wanda INEC ta bayyana wa duniya, ba daidai-wa-daida INEC ɗin ta zuba su a kwanfuta ba.
Tsohon Sanata Dino shi ne mai shaida na 22 da Atiku ya gabatar a kotu.
Lauyan Atiku Chris Uche ne ya gabatar da Melaye, wanda ya shaida wa kotu cewa shi ne ejan ɗin PDP a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe.
Ya ce ya ƙi yarda ya sa hannu kan sakamakon zaɓen da INEC ta fitar, saboda ba a zuba su cikin kwanfuta kamar yadda ya dace ba.
Ya ce ya fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓen ce tun kafin a kai ga bayyana sakamakon zabe, bayan ya gano an yi burum-burum wajen zuba sakamakon zaɓe a kwamfuta don a kayar da Atiku.
Ya ce dalili kenan yawancin ejan na PDP a faɗin ƙasar nan ba su sanya hannu kan fam mai ɗauke da sakamakon zaɓe ba, wato mai lamba EC8As.
A farkon makon nan PREMIUM TIMES Hausa ta buga cewa Atiku ya gayyaci Yakubu Shugaban INEC bayar da shaida kan shari’ar tababar nasarar Tinubu.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Mahmood Yakubu zai bayyana a Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa a ranar Alhamis, a Abuja.
Yakubu zai bayar da shaida a kan ƙarar da ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya maka Bola Tinubu, INEC da APC, inda ya nuna rashin amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, wanda Tinubu ya yi nasara.
Lauyan Atiku, Chris Uche ne ya bayyana wa alƙalan kotun su biyar bisa jagorancin Haruna Tsammani cewa Yakubu zai bayyana a kotun ranar Alhamis.
Lauyoyin Atiku ne su ka gayyaci Yakubu tare da aika masa sammacin bayyana domin ya amsa tambayoyin da za su yi masa dangane da jayayyar da Atiku ke yi kan sakamakon zaɓen.
Atiku shi ne ya zo na biyu, yayin da Peter Obi na LP ya zo na uku.
Sannan kuma lauyoyin su ka son Yakubu ya damƙa wa kotun wasu muhimman bayanan zaɓen shugaban ƙasa.
Babban Lauya Chris Uche, ya sanar da lauyoyin INEC da na APC cewa Yakubu zai bayyana a ranar Alhamis. Ya ce ya sanar da su ne don kada a kawo wani abin da zai haifar da cikas ga sauraren ƙara a ranar.
Zuwa yanzu dai Atiku ya kira masu bayar da shaida har mutum 18. Amma a ranar Talata, lauyan Atiku ya kira mai bayar da shaida na ranar da suna “Babban Mai Bada Shaida”.
Mai bayar da shaidar wato Alex Ter, lauya ne kuma tsohon Antoni Janar, tsohon Kwamishinan Shari’a na Jihar Benuwai.
Da ya ke bayani a gaban kotu, Alex Ter ya yi zargin cewa an yi gagarimin aikata rashin daidai a zaɓen shugaban ƙasa da INEC ta shirya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Ya ƙara da cewa zaɓen cike ya ke da kauce wa Dokar Zaɓe ta 2022.
A bayanin da ya yi bayan ya yi rantsuwa, Ter ya ce shi ne Kodinatan Dakin Lura da Zaɓe na PDP Situation Room) a lokacin zaɓen shugaban ƙasa, a Abuja.
Daga nan ya gabatar wa kotu da bidiyo-bidiyo da aka nuno Shugaban INEC Yakubu da Kwamishinan Wayar da Kai na INEC, Festus Okoye, su biyun su na ƙara jaddada cewa INEC za ta tura sakamakon zaɓe daga na’urar tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) zuwa Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe, wato iRev.
Kwafen bidiyo na uku da ya gabatar ya ƙunshi Shugaban Sa-ido na Kungiyar Tarayyar Turai, wanda kotun ta karɓa shi ma a matsayin shaida.
Sannan Kotun Zaɓe ta karɓi kwafen ƙa’idojin aikace-aikacen da su ka wajaba a kan jami’an zaɓe na 2022 da na 2023, a matsayin shaida duk daga hannun Alex Ter.
Ba a nan lauya Ter ya tsaya ba, ya kuma damƙa wa kotu hoton shafin Manhajar Rumbun Tattara Sakamakon Zaɓe (IReV) na INEC.
Duk da lauyoyin INEC da na Atiku sun nuna rashin amincewar su, kotun ta karɓi dukkan kwafe-kwafen bidiyon da Alex Ter ya kunna aka kalla a kotun, a matsayin shaida daga ɓangaren Atiku.
Discussion about this post