Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya gabatar wa Kotun Ɗaukaka Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa sakamakon zaɓe daga jihohi bakwai.
Obi wanda shi ne aka bayyana ya zo na uku, ya na iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen, wanda aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.
Shi ma Atiku Abubakar na PDP wanda ya zo na biyu, ya na ƙalubalantar sakamakon zaɓen.
Su biyu kowa na iƙirarin cewa shi ne ya yi nasara ba sauran ba. Kuma kowanen su na so a ƙwace nasara daga hannun Shugaba Bola Tinubu da aka rigaya aka rantsar da shi, a ɗauka a ba shi, ko kuma a sake zaɓen na shugaban ƙasa ɗungurugum.
Atiku da Obi duk sun yi zargin cewa an tafka maguɗi da ƙin bin ƙa’idojin zaɓe da su ka haɗa da bai wa Tinubu fifiko don ya tsere wa sauran ‘yan takara a zaɓen.
Rabi’u Kwankwaso na NNPP wanda ya zo na huɗu, ya bayyana cewa shi ne ma ya fi sauran ‘yan takara cancantar ya kai ƙara, amma ya haƙura saboda ba ya son ɓata lokaci.
Kwankwaso ya ce INEC ba ta buga tambarin NNPP, wato alamar da aka san jam’iyyar da ita ba, a jerin sunayen jam’iyyun da suka yi takarar zaɓen shugaban ƙasa a dukkan jerin sunayen jam”iyyun da su ka shiga takarar, lamarin da ya ce hakan ya isa kotu ta tilasta a sake wani sabon zaɓe.
A ranar Litinin da ta gabata, lauyoyin Peter Obi da su ka haɗa da Ben Anichebe da Valerie Azinge, sun gabatar wa kotu kwafe-kwafen sakamakon zaɓen jihohi bakwai na Najeriya.
Jihohin da NNPP ta damƙa sakamakon zaɓen su a kotun, sun haɗa da Ebonyi, Nasarawa, Kaduna, Imo, Ondo, Sokoto da kuma Kogi.
Nan da nan dai ita kotun ta karɓi kwafen takardun sakamakon zaɓen a matsayin shaida rubutacciya.
Sai dai kuma lauyan Tinubu, Wole Olanipekun da lauyan APC Lateef Fagbemi, duk sun yi wa kotu jayayyar ƙin amincewa da sakamakon zaɓen da Obi ya gabatar wa kotu.
Haka nan shi ma lauyan INEC sun ƙi amincewa da sakamakon da Obi ya gabatar wa kotu.
Kotu dai ta karɓi kwafen takardun, kuma ta ɗage zaman sauraren ƙarar zuwa ranar Laraba, 6 Ga Yuni domin a ci gaba da zaman.
A makon jiya ma dai Obi ya gabatar wa kotu sakamakon zaɓe na jihohi 12.
Duk da cewa Peter Obi ne ya Yi nasara a jihohin Legas, Nasarawa, Delta, Ebonyi, Imo da wasu jihohin, Obi ya ce an yi masa ƙwange an danƙara wa Tinubu ƙuri’un sa.
Discussion about this post