Majalisar Tattalin Arziki ta shawarci Shugaba Bola Tinubu da a sayar da kadarori a biya bashin da ake bin Najeriya.
Majalisar wadda ta haɗa da Tokunbo Abiru matsayin shugaba, Yemi Cardoso, Sumaila Zubairu da kuma Doris Anete.
Sun yi kira ga Shugaba Bola Tinubu cewa gwamnatin sa ta kafa tsari yadda dukkan kuɗaɗen cinikin kadarorin da za a sayar su tafi wajen biyan bashi da ake bin gwamnatin tarayya.
Sun kuma bayar da shawarar cewa a faɗaɗa kwangilar aikin samar da tsaro a Yankin Niger Delta, a ƙara jam’ian tsaro sannan a ƙara yawan ɗanyen mai da ake haƙowa a yankin.
Majalisar ta kuma bada shawara a riƙa tace ganga miliyan 2 a kullum a ƙasar nan, kuma a bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Sun kuma bada shawara a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai har miliyan 4, a cikin shekaru huɗu da za mu shiga ta wannan zango.
Sun kuma yi kira a gaggauta fara amfani da Gidauniyar Bunƙasa Yankin da ake Haƙo Ɗanyen Mai.
Ta nemi a sayar da kadarorin gwamnati a biya basussuka, sannan a gyara harkokin haƙar ma’adinai, yadda gwamnatin tarayya za ta halasta harkar, tare da cin moriyar karɓar kuɗaɗen shiga, ta hanyar halasta sana’ar.
Majalisar Tattalin Arziki ta shawarci Shugaba Bola Tinubu da a sayar da kadarori a biya bashin da ake bin Najeriya.
Majalisar wadda ta haɗa da Tokunbo Abiru matsayin shugaba, Yemi Cardoso, Sumaila Zubairu da kuma Doris Anete.
Sun yi kira ga Shugaba Bola Tinubu cewa gwamnatin sa ta kafa tsari yadda dukkan kuɗaɗen cinikin kadarorin da za a sayar su tafi wajen biyan bashi da ake bin gwamnatin tarayya.
Sun kuma bayar da shawarar cewa a faɗaɗa kwangilar aikin samar da tsaro a Yankin Niger Delta, a ƙara jam’ian tsaro sannan a ƙara yawan ɗanyen mai da ake haƙowa a yankin.
Majalisar ta kuma bada shawara a riƙa tace ganga miliyan 2 a kullum a ƙasar nan, kuma a bunƙasa tattalin arzikin yankin.
Sun kuma bada shawara a riƙa haƙo gangar ɗanyen mai har miliyan 4, a cikin shekaru huɗu da za mu shiga ta wannan zango.
Sun kuma yi kira a gaggauta fara amfani da Gidauniyar Bunƙasa Yankin da ake Haƙo Ɗanyen Mai.
Discussion about this post