Fitaccen ɗan APC kuma ɗan adawar gwamnatin Abba Yusuf ya zargi Ɗan Bilki Kwamanda ya zargi gwamnatin Kano da yi masa hassada da hanashi samun biza zuwa aikin Hajji.
Kwamanda ya ce da gangar aka hana shi biza, saboda shi ɗan adawa ne ɗan jam’iyyar APC.
” Duk wani da aka saka a cikin wadanda za su yi wa alhazan Kano hidima a saudiyya, wannan gwamnati ta cire su, mutum kusan 150 saboda ba ƴan Kwankwasiyya bane.
Kwamanda ya ce duk an canja su da ƴan Kwankwasiyya.
” A Abuja na biya kujeru na, amma sai na ce ta Kano zan tashi. Da na zo Kano sai suka hana ni biza
Sai dai kuma Hukumar Alhazai ta jihar Kano ta karyata waɗannan zarge-zarge in da suka ce ba da biza ba hurumin hukunar alhazan Kano bane, saboda haka shi ya san inda ya baro bizar sa amma ya dai na ƙala wa ko ɗora wa jihar laifin rashin samun biza.
Discussion about this post