Gwamnan Kaduna Uba Sani ya zargi gwamnonin yankin Arewa-Maso-Yammacin Najeriya da suka shude da ruruwa tsananin rashin tsaro da ake fama da shi a yankin.
Uba Sani ya bayyana haka a lokacin da yake hira da Talabijin din Channels ranar Talata.
Yankin Arewa maso Yamma dai na fama da hare-hare daga wasu ‘yan ta’adda da ake yi wa lakabi da mahara ko ‘yan bindiga. Su na fasa garuruwa da kauyuka suna kashe mutane, su sace wasu sannan su kwashe musu dukiya.
Ban da jihar Kaduna, jihohin Jigawa, Kano, Katsina, Kebbi, Sokoto da Zamfara duk sun fada hannun irin wadannan mutane.
Sanata Uba Sani ya ce ” Sakaci da nuna halin ko in kula daga gwamnonin da suka wuce ne ya sa aka fada cikin mummunar yanayi na rashin tsaro a ayankin Arewa Maso Yamma.
” Tun ina majalisa, na fito na fadi karara cewa matakan da gwamnonin yankin da suka dauka ne ya ruruta wannan bala’i na rashin tsaro a jihohin da ake fama da shi. Sam ba su yi yadda ya kamata su yi ba don kawo karshen wannan balai na ‘yan bindiga da ya hallaka mutanen mu.
Gwamna Uba ya kara da cewa ” A baya gwamnonin yankin Arewa Maso Yamma tare da jihar Neja, sun yi tsari yadda zasu yi maganin abin. Sun amince su bude wata asusu domin kafa amfani da kudin wajen yaki da rashin tsaron, amma da gamngar kowa ya kama gaban aka banzatar da abin.
” Hakan bai yiwu bane, a lokacin da wasu gwamnonin suka kama gaban su, suka rika gayyatar gaggan shugabannin ‘yan bindigan suna shan shayi da su a teburi daya. Suna dankara musu makudan kudi suna sallamar su. Mu ba mu amince da wannan tsari ba shi yasa gaba dayan abin bai yi tasiri ba.
Inda muka dosa yanzu
Gwamna Uba Sani ya ce a cikin wannan mako ya gana da sabbin gwamnonin da aka rantsar, domin su dawo teburin tattauna yadda za su tunkari abin cinkin gaggawa ba tare da an bata lokaci ba.
“Mun amince cewa dole ne mu samar da tsarin bai daya kan lamarin. Kuma dole ne mu kauce daga matakin da wasu gwamnonin da suka shude suka dauka na yin sulhu da yan bindigan a baya a lokacin da suka fara b dankara musu kudi ana tattaunawa da su.
” Amma yanzu dukkan mu mun amince za mu yi aiki tare, tare da gwamnan Neja wanda duka jihohin sun yi iyaka da jihar domin tunkarar matsalar kai tsaye.
A karshe ya ce duka gwamnonin sun tsara hanyoyi na bai daya wanda za su bi domin fatattakar wannan matsala da yaki ci yaki cinyewa a yankin.
Discussion about this post