Wani masani kan tattalin arziki mai suna Abiola Metilelu, ya ce akwai buƙatar tilas a yi wa Dokar Lamunin Ɗaliban Manyan Makarantu kwaskwarima.
Ya ce tsauraran sharuɗɗan da ke tattare da tsarin zai hana ɗalibai samun damar amfana da tsarin.
Masanin shi ne Shugaban Kamfanin PressPayNG, sun ƙware wajen baiwa ɗalibai shawarar yadda za su riƙa biyan kudin makarantar su a sauƙaƙe.
Ƙwalelen Ramcen Kuɗaɗe: Tsauraran Ƙa’idojin Da Ɗalibai Ba Su Iya Cikawa:
Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani.
1. Wannan shiri ya na ƙarƙashin wata doka da Shugaba Bola Tinubu da sa wa hannu a ranar Litinin, mai suna ‘Access to Higher Education Act’, 2023. Wato Dokar Samun Damar Ɗalibi ya kai matakin Ilmin Gaba da Sakandare, ta 2023.
2. Shi wannan lamuni babu kuɗin ruwa a cikin sa.
3. Duk wanda ya karɓi lamunin ba zai fara biya ba, sai bayan shekaru biyu da kammala NYSC ɗin sa.
4. Gwamnati za ta riƙa tara kuɗaɗen da za ta riƙa bai wa ɗalibai ramce ta hanyar gimtsar kashi 1% na ribar ɗanyen mai da dukkan albarkatun ƙasa waɗanda gwamnati ke samun kuɗaɗen shiga a ƙarƙashin su. Sai kuma kashi 1% na dukkan kuɗaɗen shigar da Hukumar Tara Kuɗaɗen Shiga ta Ƙasa, FIRS ke tarawa.
Sai kuma wani kashi 1% daga kuɗaɗen da Hukumar Shigi da fice ke tarawa, wanda Hukumar Kwastan ke tarawa da kuma na Fannin Harkokin Ilmi.
5. Haka kuma gwamnati za ta riƙa karɓar kyauta, agaji, tallafi da hasafin kuɗaɗe daga wurare daban-daban don ta riƙa bai wa ɗalibai ramce.
6. Za a riƙa killace kuɗaɗen a Babban Bankin Najeriya, CBN ana kamfata ana bayarwa bashi ga ɗalibai.
8. Kwamiti ne zai riƙa lura da kuɗaɗen, mai ƙunshe da mutum 11, a ƙarƙashin shugabancin Gwamnan CBN.
9. CIkin ‘yan kwamitin zai kasance akwai Gwamnan CBN, Ministan Ilmi, Ministan Kuɗaɗe da Odita Janar na Tarayya. Sai Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i (NUC), Wakilin Shugabannin Jam’i’o’i da na Manyan Makarantu.
11. Akwai wakilin NLC, NBA da na ASSU.
Su Wa Za Su Iya Cin Gajiyar Lamunin?:
12. Sai ɗaliban jami’o’i, kwalejin fasaha da makarantun koyon sana’a waɗanda gwamnati ta kafa.
13. Sai ɗalibin da abin da iyayen sa ke samu a shekara bai kai Naira 500,000 ba.
14. Sai ɗalibi ya kai sunan garanto biyu, waɗanda muƙamin su aƙalla ya kai matakin albashi na 12, sai lauya wanda aƙalla ya kai shekaru 10 ya na aikin lauya. Idan ba lauya, to a samu ma’aikacin kotu.
15. Ba za a ba ɗalibin da aka taɓa kamawa ya yi satar jarabawa ba, ko wani gagarumin laifi.
16. Wanda ya ƙi biyan bashin zai iya fuskantar tara ta N500,000, ko ɗaurin shekara biyu a kurkuku.
17. Mai buƙatar bashin zai cika fam a banki zuwa da Kwamitin Kula da Kuɗaɗen Ramcen Ɗalibai, kai tsare ga Gwamnan CBN.
18. Kwana 14 bayan cika fam za a sanar da ɗalibi idan zai samu, ko a’a.
Discussion about this post