Akalla mutum 13 ne suka rasa ran su a makon jiya a dalilin rikicin da ya barke tsakanin makiyaya da manoma a karamar hukumar Barkin Ladi jihar Filato.
Wannan rikicin ya biyo bayan kisar makiyaya biyar da aka yi a kauyen Rawu ranar Alhamis din makon jiya.
A ranar Juma’an da ya gabata wasu mahara da ake zaton makiyaya ne sun kashe mutum takwas.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Alabo Alfred bayan ya tabbatar da kisar makiyaya biyar din da aka yi ya ce bashi da masaniyar cewa an kara kashe wasu mutum 8 ranar Juma’a.
“Ban da masaniyar an kashe wasu mutum 8 ranar Juma’a amma ina da da masaniyar kisan mutum biyar din da aka yi a kauyen Rawu inda a wannan hari an kona gidaje masu yawa.
Bayan haka Shugaban kungiyar Miyetti Allah na Kasa MACBAN Nuru Abdullahi ya bayyana wa jaridar ‘Dailiy Trust’ ranar Juma’a cewa a ranar Juma’ar makon jiya an kama wasu makiyaya biyar a lokacin da suke dawowa daga kiwon dabobbin
Discussion about this post