Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa duk da dai shi a zuciyar sa akwai waɗanda ya fi so su kasance shugabanni a Majalisar Dattawa da ta Wakilai ta Ƙasa, duk da haka a shirye ya ke a yi aiki tare da ko ma su wa aka zaɓa su ka zama shugabanni.
Tinubu ya yi wannan furuci a ranar Juma’a, a lokacin da ya ke ganawa da Sarakunan Gargajiya na Najeriya a Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja.
Sai dai kuma ya yi kira ga Sarakunan Gargajiya da su shawarci zaɓaɓɓen wakilan kada su fifita son ran su.
“Shugaban Ƙasa ya yi kira ga sarakunan gargajiya cewa su shawarci wakilan su kada su yi amfani da son ran su wajen zaɓen shugabannin majalisa. Ya ce akwai bukatar a samar da kyakkyawar majalisar da za a riƙa aiki tare ba tare da yawan haifar da ruɗun da ba shi da wani alfanu ga ci gaban Najeriya ba.
Daraktan Yaɗa Labarai na Fadar Shugaban Ƙasa, Abiodun Oladunjoye, ya ƙara da cewa, “Tinubu ya ce a shirye ya ke da ya yi aiki tare duk waɗanda aka zaɓa shugabanni a Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai ta Ƙasa, wato ta Tarayya. Ya ce ci gaban Najeriya shi ne abu mafi muhimmanci a wurin sa.”
“Tilas mu tashi tsaye mu tabbatar da ɗorewar Najeriya. Tilas mu tashi mu ciyar da Najeriya gaba. Tilas Najeriya ta bunƙasa.” Inji Tinubu.
Tinubu da APC sun zaɓi Godswill Akpabio da Barau Jibrin a matsayin Shugaba da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa. Yayin da a Tarayya kuwa, sun zaɓi Tajuddeen Abbas da Ben Kalu a matsayin Kakakin Majalisar Tarayya da Mataimakin Kakakin Majalisar Tarayya.
Sai dai kuma hakan bai hana fitowar wasu ‘yan takarar ba.
Discussion about this post