Kamfanin Siminti na BUA Cement PLC, mallakar hamshaƙin attajiri Abdussamad Isyaka Rabi’u, ya karɓo lamunin Dala Miliyan 500 daga Gamayyar Cibiyoyin Hada-hada na Duniya (IFC).
BUA zai yi amfani da kuɗaɗen don samar da wadataccen siminti ta hanyar inganta wutar lantarki a masa’antar siminti wadatacce a Arewa.
A cikin wata sanarwa BUA ya fitar, ya ce wannan haɗin-guiwa da IFC ya yi da BUA, ita ce mafi girman haɗin-gwiwar zuba jari da ya yi, wanda hakan zai samar wa matasa aƙalla 12,000 aiki da kuma bunƙasa ci gaba a Najeriya, har ma da ƙasashen yankin Sahel.
Sanarwar ta ce Cibiyar IFC ce za ta samar da kuɗaɗen har Dala Miliyan 500, waɗanda a cikin kuɗaɗen, lamuni ne na Dala Miliyan 160.5 daga Asusun Bankin IFC. Akwai kuma Dala Miliyan 94.5 da za su fito daga Cibiyar Bayar da Lamuni Ga Manyan Masana’antu ta MCPP. Sai kuma dala Miliyan 245 da wasu cibiyoyin hada-hadar maƙudan kuɗaɗe da su ka haɗa da Bankin Raya Ƙasashen Afrika (AfDB), shi kuma zai bai wa BUA dala miliyan 100, sai AFC da zai bayar da Dala Miliyan 100 shi ma dala miliyan 100, sai mashahurin kamfanin hada-hadar inshora na Jamus, wato Deutsche Investitions shi kuma zai bayar da dala miliyan 45.
BUA ya yi wannan sanarwa ce a Abidjan, wurin Taron Ƙungiyar Hamshaƙan Attajiran Afrika Masu Manyan Kasuwanci a duniya.
Idan BUA ya narka kuɗaɗen a kasuwancin sa, to zai kasance shi ne na biyu wajen samar da siminti a Masana’antar Simintin sa da ke Sokoto.
Ya ce masana’antar za ta yi aiki ne da man da ake samu daga taki sai kuma hasken sola.
Kowane zai riƙa samar da tan miliyan uku na siminti a duk shekara. Zai riƙa samar da siminti a Najeriya, Nijar da Burkina Faso.
Discussion about this post