Hasalallun matasa a Kano sun yi Riga Malam Masallaci, inda suka afka wa shagunan ƴan canji dake ginin tsohuwar jaridar Triumph dake Kano.
Matasa sun diran ma wannan gini suka fara diban kayan jama’a waɗanda basu ji ba basu gani ba.
Duk da cewa gwamnati ba ta kai ga rusa waɗannan gina ba, matasa sun yi gaban kan su sun afka ginin sun fara diban ganima.
Wakilinmu ya lura da yadda masu shaguna da kadarorin da gwamnatin Ganduje ta sayar da su ke kwashe kayansu saboda fargabar kada gwamnati ta ruguza gine-ginen cikin dare a ci gaba da rusa ginin da sabuwar gwamnatin ke yi.
Haka kuma a ranar Asabar gwamnati ta rusa wani gini mai hawa uku mai shaguna 90 da ke Nasarawa.
Tun daga wannan rana ta Asabar, matasa suka fara jidar kayan gini da aka rusa da dukiyoyin mutane da sunan ganima.
Sabuwar gwamnatin Kano ta rusa wasu shaguna da tsohon gwamnan Kano, Ganduje ya siyar wa ƴan kasuwa.
Jama’a da dama dun yi tofin Allah-wadai da wannan aiki da gwamnati ta sa a gaba. Wasu kuma na ganin gwamnati ce kowa ya samu rana yayi shanya.
Discussion about this post