Tsohon shugaban hukumar EFCC, kuma mataimakin Sufero Janar ɗin ƴan sanda mai ritaya, Nuhu Ribadu ya bayyana cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta kakkabe ta’addanci a Najeriya, ta maido da zaman lafiya na dindindin a kasar.
Ribadu ya bayyana haka a lokacin da yake jawabin soma aiki a matsayin babban mai baiwa shugaban kasa shawara ta musamman kan harkar tsaron kasa.
A yau Litinin ne Ribadu ya amshi ragamar shugabanci a wannan ofis na NSA daga hannun Janar Babagana Monguno mai ritaya.
” Za mu daidata kasar nan, za mu kare kasarmu, kuma za mu tabbatar da dawwamammen zaman lafiya a Najeriya, domin mun yi imanin cewa lokaci ya yi da kasar nan za ta samu zaman lafiya mai dorewa, da dawo da bin doka da oda kamar kowace kasa a duniya.
” Tabbatar da tsaro a ƙasa babbar aba ce. Ba abune da za a rika wasa da shi ba. Za mu duba abinda aka yi a baya domin mu dora akai. Rokon da muke yi gare ku shine ku ba mu haɗin gwiwa yadda ya kamata.
” Burin shugaba Tinubu shine ya ga an kawo karshen ta’addanci da matsalar tsaro a faɗin kasar nan. Wannan shine burin sa kuma InshaAllah za mu haɗu don cimma haka.
A karshe Ribadu ya ce aikin samar da tsaro a kasar nan aba ce da ke neman haɗin kan kowa da kowa a nan kasa Najeriya da ma abokan huldan mu na waje duk baki ɗaya.
Discussion about this post