Ƴan Najeriya sun ƙara shiga ruɗanin tarangahumar canjin kuɗi a ranar Laraba, yayin da Kotun Ƙoli ta ƙara ɗage sauraren ƙarar da Gwamna Nasiru El-Rufai, Yahaya Bello da Bello Matawalle su ka kai, dangane da wa’adin ranar daina amfani da tsoffin kuɗaɗe ta 10 ga Fabrairu.
An ɗage ƙarar zuwa ranar 22 ga Fabrairu, wanda a tunanin mutane a ranar Laraba ɗin ce ya kamata a yanke hukunci, saboda muhimmancin batun da ake tankiyar a kan sa.
Babban Bankin Najeriya ya jefa jama’a cikin matsanancin ƙarancin kuɗi, bayan ya karɓe naira tiriliyan 2.1 daga hannun su, amma kuma ya buga sabbin kuɗaɗe naira biliyan 300 kacal. Amma kuma wai bankin na nan ya na haƙilon ƙara buga naira biliyan 200, waɗanda ba wata isar jama’a yin hada-hadar yau da kullum za su yi ba.
Yayin da matsi da ƙuncin rayuwa ya tsananta, ana ci gaba da samun rahotannin mutuwar marasa lafiya, saboda sun kasa cirar kuɗin su a banki har su sayi magani. Kuma mun ga yadda maza da mata ke harzuƙa har su tubure su yi tsirara a cikin bankuna, don dai a biya su kuɗin su.
Jihohi irin su Lagas, Bayelsa, Edo, Ondo, Sokoto, Cross River da Ekiti duk sun shiga sahun Kano, Kogi da Zamfara sun maka CBN da Shugaba Buhari ƙara a Kotun Ƙoli.
Yayin da Godwin Emefiele ya ƙi bin umarnin kotu, haka shi ma Shugaba Muhammadu ya yi fatali da umarnin kotu, sai ya fito a ranar Alhamis ya ce a ci gaba da karɓar naira 200 har nan da ranar 10 Ga Afrilu, kwanaki 60 kenan.
A jihohi da dama kuma an tarzomar da ke kai ga ana ƙone bankuna ko na’urar ATM.
Ya kamata a kula da cewa yin fatali da dokar ƙasa bin wata hanya ko turba ce wadda ba ita ba ce mafita. Irin wannan hanya Emefiele ya bi, kuma kamata ya yi a taka masa burki.
Kunnen-ƙashin da CBN ya yi ya tsaida ƙananan kasuwanci na masu sana’o’in yau da kullum. Haka direbobin motocin sufuri da sauran masu sana’o’i, saboda daina karɓar tsoffin kuɗaɗe, alhali sabbin ba su wadata ba.
Hakan jawabin Shugaba Buhari ma ya yi fatali ne da Kotun Ƙoli, domin ya yi riga-malam-masallaci ya ce a daina hada-hada da naira 500 da 1000, alhali Kotun Ƙoli ba ta kai ga yanke hukunci ba tukunna.
An wayi gari yanzu a ƙasar nan gwamnati na tunzira jama’a su far mata.
Emefiele da CBN su daina raina wa mutane wayau, su na cewa wai ƙarar da gwamnoni su ka shigar ba a saka sunayen su ba.
Emefiele ba shi da hurumin da sai ya zaɓi umarnin kotun da ya ga dama sannan zai bi.
Matsalar banki a ƙasar nan ta na da yawa. Gwamna Abdullahi Ganduje na Kano, ɗaya daga cikin waɗanda su ka garzaya kotu, ya ce ƙananan hukumomi 24 daga cikin 44 na Kano duk ba su da bankuna. Daga cikin ƙanananomi 17 a jihar Yobe, 4 ne kawai ke da bankuna.
Shi kuwa Salihu Lukman, Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC cewa ya yi akwai ƙananan hukumomi 300 a Arewa gaba ɗaya waɗanda ba su da bankuna. Shin ta yaya mutanen da ke zaune waɗanda yankunan za su iya gudanar da harkokin su?
Ya kamata Buhari da Emefiele su naɗe tabarmar kunya su dakatar da wannan makahon tsarin kuɗin da su biyu kacal su ka ƙirƙiro wa mutum sama da miliyan 200 a ƙasar nan.
Ko a cikin makon da ya gabata sai da wannan jarida ta bayyana ra’ayin ta, inda ta nanata cewa: A gaggauta ceto Najeriya daga hannun Emefiele, ɗan ragabza da gidoga.
A cikin ra’ayin, Premiium Times ta nuna cewa duk wani abin da ya biyo bayan sauya launin kuɗi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya yi, ba abin mamaki ba ne, domin tun farko sai da masu hankali da hangen nesa su ka yi tsinkayen faruwar hakan.
Jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin halin ƙarancin sabbin kuɗaɗe bayan an raba su da tsofaffin da ke hannun su an kimshe a banki, ya haifar da gagarimar matsalar da ta kai har hasalallu na ƙona gine-gine har da bankuna.
Daga cikin abin da ya harzuƙa mutane su ka fara ɗaukar doka a hannun su, har da tinzirawar da CBN ya Yi masu, inda ya ce bankunan kasuwanci ne ke ɓoye sabbin kuɗaɗe ba su son bai wa kwastomomin su.
Rabuwar kawuna da saɓani tsakanin Shugaban Ƙasa da Gwamnoni ta yi tsamarin da har wasu sun garzaya Kotun Ƙoli sun maka shi kotu, su na neman kotu ta tilasta wa CBN ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe, tunda sabbin ba su wadata ba.
Babban abin tsaro dangane da wannan giribtu da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya yi na hana kuɗaɗe kewayawa a hannun ƙananan yan kasuwa da sauran masu sayen kayan buƙatun yau da kullum, wata illa ce wadda za a daɗe nan gaba ba a magance ta ba.
Tuni har an ma fara hasashen cewa an yi asarar kashi 3 bisa 100 na tattalin arzikin ƙasa a cikin ‘yan kwanakin nan. Kafin canjin kuwa har ana murnar cewa Najeriya za ta samu bunƙasar tattalin arzikin ƙasa da kashi 3.2 bisa 100 a 2023, kamar yadda Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya yi hasashe.
Abubuwa masu matuƙar hatsari da barazana sun faru kan tattalin arzikin Najeriya da ita kan ta zamantakewar ƙasar, waɗanda kuma barazana ce ga zaɓen 2023.
Idan za a iya tunawa, tun daga lokacin da Emefiele ya tsoma dungulmin yatsun sa cikin siyasa, wannan jarida ta fito ba sau ɗaya ba, ta yi kiran ya sauka daga shugabancin CBN, ko kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shi. Kuma tun daga lokacin ne duk mai hangen nesa zai iya fahimtar cewa wannan ɗan ragabza da gidoga bai damu da da kiyaye dokokin aikin sa na shugabancin CBN ba, harankazamar sa kawai ya ke yi, duk kuwa da an san hakan babbar barazana ce ga ƙasar nan.
Saboda haka, Gwamnonin Najeriya sun yi gaskiya da su ka fito a ranar Lahadi su ka ce, “ƙwacen kuɗaɗe Emefiele ya yi wa jama’a, ba canji ko musayar kuɗaɗe ba.”
Tulin kuɗaɗen da ke zagayawa ana hada-hada da su a hannun jama’a, ba su ne ke kawo tsadar kayan masarufi, abinci da tsadar rayuwa ba. Abin da ke tsayar da tsadar farashi shi ne CBN ta gindaya ƙa’ida ko geji na canjin kuɗaɗen waje.
Idan aka kalli yadda masu tarzoma su ka riƙa ragargaza ginin bankuna su na gaggaɓe ƙofofin bankuna ko fasa na’urar ATM wurin neman a maido masu kuɗaɗen su a hannu, hakan ya isa a gane tsarin da Emefiele ya shigo da shi ba mai karɓuwa ko yin tasiri ba ne a cikin jama’a.
Rainin wayo da tunzira jama’a fa Emefiele ya yi, ya ce wai bankunan kasuwanci su ka ɓoye sabbin kuɗaɗe. Amma da ya sha matsa kamar gyaɗa, sai a fito ya faɗi gaskiya, ya ce ba a buga wadatattun sabbin kuɗaɗen da jama’a ke buƙata ba.
Idan aka dubi irin asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi, sai kuma la’akari da halin ƙuncin da miliyoyin mutane ke ciki, babu sauran wata hujja ko dalilin da wani zai kawo domin ya kare wannan wawanci da Emefiele ya ɗibga.
Shin yanzu akwai wani maras kunyar da zai iya fitowa ya kare Emefiele ya ce bai cancanci a tsige shi ba? Tsige Emefiele shi ne alheri kuma yin hakan ne zai zama ruwan kashe dafin gubar da ya dasa a ƙasar nan.
Discussion about this post