Shugaba Bola Tinubu ya yi namijin cire tallafin fetur, a ranar da aka rantsar da shi, lokacin da ko zama ofishin sa bai kai ga yi ba.
Ko ba komai dai a waccan rana ta 29 ga Mayu, sanarwar alama ce da ta nuna za a yi bankwana da wani alaƙaƙai da ya dabaibaye ‘yan Najeriya da tattalin arzikin ƙasa tsawon shekara da shekaru da sunan tallafin fetur.
Cire tallafin ya yi wa Bankin Duniya da Bankin Bada Lamuni na Duniya daɗi ainun, tunda dama sun daɗe su na bayar da shawarar a cire shi kawai.
Amma dai su talakawa da faƙirai da marasa galihu, lamarin bai yi masu daɗi ba, domin su ba su san wani alfanun cire tallafin ba, sai masifar tsadar rayuwar da ke tattare da shirin kaɗai su ka sani. Wato dai kamar yadda Bahaushe ke cewa “ruwan da ya doke ka, shi ne ruwa.”
Cire tallafin fetur tsari ne wanda zai ceto Najeriya daga ƙangin durƙushewa da talaucewa. Tsarin ya kawo ƙarshen kamfatar kuɗaɗen da shugabanni marasa kishi su ka riƙa yi, su na biyan wasu marasa kishi da sunan tallafin fetur, sama da shekaru 30.
Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC) ba ta yi laifi ba da ta nuna wa gwamnatin tarayya rashin amincewar ta, saboda ba a yi shawara ba aka yi gabagaɗin cire tallafin. Sannan kuma ba a bijiro hanyoyin sauƙaƙa wa jama’a tsananin ƙarin fasashin da za su riƙa fuskanta ba.
Dama ita ƙungiyar ƙwadago ta TUC tuni ta bijiro wa gwamnatin tarayya da uzirin neman a maida mafi ƙanƙantar albashi ya zama Naira 200,000, maimakon Naira 30,000. Hakan kuma ita ma NLC ta amince da adadin ƙarin.
To tuni dai ƙasar nan baki ɗaya an yi ittifaƙin cewa tallafin fetur kawai wani salon damfara ce a gwamnatance.
Haka kawai ana biyan wasu riƙaƙƙun ‘yan damfara kuɗaɗen da su ka kamata a ce an yi wa jama’a ayyukan inganta rayuwar su da kuɗaɗen tsawon shekaru masu yawan gaske. Gwamnatocin baya sun kasa samun ƙwarin guiwar cire tallafin fetur, shi ya sa su ka dawwama a ƙarƙashin garken baragurbin da ke sace kuɗaɗen ƙasar nan.
Gaggawar da Tinubu ya yi ya cire tallafin fetur, abu me mai kyau. Zai ɓamɓare mu daga mummunan halin da gwamnatocin baya su ka jefa mu cikin halin ni-‘ya-su.
Dama kuma ko a zaɓen 2023, manyan ‘yan takarar shugaban ƙasa duk ba su yarda da tallafin fetur ba. Wato Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP da shi kan sa Tinubu na APC.
Tallafin fetur asara ce, zamba ce, kuma walle-walle ne. A cikin shekaru 20 an kashe dala biliyan 25 wajen gyaran matatun mai na Fatakwal, Warri da na Kaduna ɗin. Amma lalatattun manyan jami’ai ‘yan gidoga sun karkatar da kuɗin, har yau ba a gyara matata ko ɗaya ba. Wannan kuma abin kunya ne ga Najeriya, ƙasa mai ƙasaitaccen arzikin ɗanyen man fetur a duniyar OPEC.
Daga biyan naira bilyan 257 na tallafin ɗanyen mai a 2006, a 2022 an ce an biya Naira tiriliyan 8.7 kuɗin tatyafin fetur.
Sannan fetur ɗin da Jamhuriyar Nijar, Chadi, Kamaru, Ghana, Togo da Jamhuriyar Benin ke sha, duk wanda aka cire wa tallafi ne daga Najeriya. Asara goma da ashirin kenan ga Gwamantin Tarayya.
Wata matsalar kuma ita ce yadda Gwamantin Tarayya ke kamfatar kashi 96% bisa 100% na kuɗaɗen shigar ƙasar ta hanyar biyan basussukan da ake bin Najeriya, wanda adadin kuɗaɗen sun kai Naira tiriliyan 77.
Kamata ya yi a ce tun watanni 18 da su ka gabata aka kawo ƙarshen tallafin fetur, lokacin da aka sa wa Dokar Fetur ta 2021 hannu.
Ko ma dai me kenan, cire tallafin fetur daidai ne. Amma lamarin ba zai saisaita ba, har sai Tinubu ya ƙara da daƙile rashawa da cin hanci da kuma ƙwato makudan kuɗaɗen da barayin gwamanti su ka sata a baya.
Discussion about this post