• PREMIUM TIMES |
  • Tallata Hajar ka |
  • Adireshin mu |
  • PTCIJ |
  • Dubawa
Premium Times Hausa
  • Labarai
    • All
    • Duniya
    Ƴan sanda sun damke wasu abokai ƴan kungiyar matsafa dake tsafi da kawunan mutane a Ilori

    Yadda ƴan sanda suka kama Ibrahim da ya yi garkuwa da Fatima, ya ƙarɓi kuɗi kuma ya yashe ta a Zariya

    Kotu ta kori gwamna Sule na Nasarawa, ta ce PDP ce ta yi nasara a zaɓen gwamna

    Ku fito ku ceci mutanen jihar Kaduna kamar yadda kuka yi a zaben majalisun Tarayya da na sanatoci – Isah Ashiru

    An yi mana kwange a hukuncin kotu, za mu daukaka kara – Ashiru

    SSS

    TAKE HAƘƘIN ƊAN ADAM: Yadda SSS suka riƙa faffalla min mari, suka ja ni ƙasa girrrr, don kawai na ce su bi doka – Lauya Ogbankwa

    Muna ƙarancin malamai, a janye dokar hana ɗaukar sabbin malamai da gwamnatin tarayya ta ƙaƙaba – Jami’ar ABU

    TONON ASIRI: An kama wani Dagaci cikin gungun mahara a lokacin batakashi da ‘Yan sanda

    ‘Yan bindiga sun kashe mutum shida a Kaduna

    Almajirai

    UNICEF ta saka Almajirai sama da 20,000 cikin rajistar tsarin agaza wa marasa karfi a Katsina

    Majalisar Tarayya ta ce a soke ƙarin kuɗin makaranta da aka yi wa ɗaliban jami’o’i da na Kwalejojin Gwamnatin Tarayya

    KALUBALEN DA KE GABAN MAJALISAR WAKILAI TA ƘASA: Gaganiya da matsalar raɗaɗin tsadar rayuwa, matsalar tsaro da sauran su da ake fuskanta a kasa

    Yadda sojojin sama sun ragargaza sansanonin ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Sokoto da Kaduna

    RASHIN TSARO: Tinubu ya amince da sayo jiragen sama masu saukar ungulu 12 ga sojojin Najeriya – Lagbaja

  • Labarai daga Jihohi
  • Wasanni
    Hukumar CAF za ta binciki yadda mahaifiyar ɗan wasa ta mutu cikin 1986, shi kuma ya ce atabau cikin 1990 ta haife shi

    A karo na Uku, Moroko za ta ɗauki baƙuncin gasar cin kofin kwallon ƙafa na nahiyar Afrika a Janairun 2025

    NFF ta sake nada Chris Danjuma a matsayin kocin Falconets

    DARAJAR ƘWALLON ƘAFA TA KOMA SAUDIYA: Karim Benzema zai riƙa ɗaukar albashin kusan Naira Biliyan 100 a shekara, a ƙungiyar Al-Ittihad

    TSOHO MAI RAN ƘARFE: Obasanjo ya zura ƙwallaye uku a wasan sada zumuntar tsoffin ɗaliban sakandare

    QATAR 2022: Yadda Croatia, ƙasa mai mutum miliyan 4 ta kori Brazil ƙasa mai mutum miliyan 216

    AMBALIYAR QATAR 2022: Spain ta kori kociya Luis Enrique bayan ta kwashi buhun kunya a hannun Marocco

    QATAR 2023: Yadda Walid, kociyan Morocco ya rikita duniyar ƙwallon ƙafa cikin watanni 4 kacal

    QATAR 2022: Dukkan ƙasashen Afrika 4 da su ka taɓa kai wasan kaiwa ga na kusa da na ƙarshe, su na da tauraro a jikin tutocin su

    Abubuwan al’ajabi dangane da fatattakar da Morocco ta yi wa Spain daga Qatar 2022

  • Kiwon Lafiya
  • Nishadi
  • Bidiyo da Hotuna
    BIDIYO: Yadda rufe iyakar Najeriya da Nijar, ya jefa mu cikin tsananin fatara, da halin kakanikayi a yankin Katsina – Saidu

    Yadda SSS da Jami’an Gidan Kurkuku suka kwashi ‘yan kallo a kotu, saboda Emefiele

    BIDIYO: ‘Duk wanda ya ci kuɗin Tallafin Korona a Jigawa sai ya amayo shi’ – Gwamna Namadi

    BIDIYO: ALhazan Kano sun gama shiri tsaf don ‘Hawan Arafat’ – Alhussain Maiwada

    JERIN SUNAYE: Jami’o’i 51 da ba za su dauki dalibin da ya ci kasa da maki 180 a jarabawar JAMB ba

    TSARIN BAI WA ƊALIBAI RAMCE: Abubuwan da suka wajaba ɗalibai da iyaye su sani

    Buhari ya tashi zuwa Saudiyya, zai yi Umra ta ƙarshe a matsayin sa na shugaban kasa

    BIDIYO: Buri da fata na a 2023: Ra’ayoyin jama’a

    BIDIYO: Ƙogon Al’ajabi, ƙogon Waraka, Ƙogon biyan bukata a jihar Enugu

    Mutanen Arewa na da alƙawari da sanin ya kamata, Tinubu za su yi saboda ƙauna da biyayyar da ya nuna wa Buhari – El- Rufai

No Result
View All Result

RA’AYIN PREMIUM TIMES: Buƙatar korar Emefiele daga CBN da kuma yi wa bankin garambawul

Premium Times HausabyPremium Times Hausa
June 5, 2023
in Babban Labari
0
RA’AYIN PREMIUM TIMES:  A gaggauta ceto Najeriya daga hannun Emefiele, ɗan ragabza da gidoga

A kusan ƙarshen wa’adin gwamnatin Buhari, PREMIUM TIMES ta riƙa yin kakabin kiraye-kirayen Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sauka daga muƙamin sa, sannan a gurfanar da shi kotu, kuma a garƙame shi.

Godwin Ifeanyichukwu Emefiele ya tafka rashin gaskiya ta hanyoyi da dama. Kama daga bai wa gwamnatin Buhari ramcen Naira tiriliyan 23.2 zuwa sauya launin kuɗaɗen ƙasar nan. Duk waɗannan laifuka ne na yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-ƙasa.

Amma kasancewar Emefiele ya ci gaba da zama Shugaban CBN har bayan saukar Buhari, wato har cikin mulkin Bola Tinubu, hakan tabbas ya nuna irin riƙon da ba mu yi wa ladaftar da waɗanda su ka ɗibga cin amanar ƙasa.

Dalili kenan jami’an da ba su cancanta ba su ke ci gaba da kasancewa bisa manyan muƙaman da aka ɗora su, maimakon su sauka saboda abin kunya da takaicin da su ka ɗibga.

Garambawul ɗin da ake so a yi wa fasalin tattalin arzikin Najeriya, ba abu ne mai yiwuwa ba, matsawa Emefiele wanda shi ne ruguzau ɗin da ya ruguza tattalin arzikin ya na kan muƙamin sa.

Mummunan yanayin da asusun gwamnatin tarayya ke ciki, musamman yadda babu komai cikin sa sai tulin bashi da tsadar rayuwa, ya kai ga Najeriya har ta ƙurar malejin ta na gejin bashin da ake bi.

Ya zama tilas sabbin shugabannin CBN masu zuwa nan gaba su yi wa fasalin CBN garambawul, tare kuma da yin ƙwaƙƙwaran bincike kan ayyukan asshan da aka tafka a CBN tsawon shekaru takwas.

PREMIUM TIMES na so a bayyana yadda CBN ya riƙa bai wa Najeriya kuɗaɗe ta na cike giɓin kasafin kuɗi har tsawon shekaru takwas a jere, kuɗin da sun doshi tiriliyan 14.

Akwai buƙatar a gyara tsarin yadda ake naɗa Gwamnan CBN. Wannan garambawul kuwa ya haɗa har da daƙile irin yadda Emefiele ya riƙa yin hawan ƙawara kan wasu ƙa’idoji ya na haifar wa tattalin arzikin ƙasar nan gagarimar matsala.

Haka nan akwai bukatar yin gyara kan yadda ake naɗa mataimakan shugaban babban bankin Najeriya, CBN. Akwai batun buƙatar naɗa mataimakan gwamnan CBN su shida, don kula da shiyyoyi shida.

Wani ra’ayi na baya da PREMIUM TIMES ta yi kan gwamnan babban bankin Najeriya, jaridar ta nemi a gaggauta ceto Najeriya daga hannun Emefiele, ɗan ragabza da gidoga.

Duk wani abin da ya biyo bayan sauya launin kuɗi da Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya yi, ba abin mamaki ba ne, domin tun farko sai da masu hankali da hangen nesa su ka yi tsinkayen faruwar hakan.

Jefa ‘yan Najeriya cikin mawuyacin halin ƙarancin sabbin kuɗaɗe bayan an raba su da tsofaffin da ke hannun su an kimshe a banki, ya haifar da gagarimar matsalar da ta kai har hasalallu na ƙona gine-gine har da bankuna.

Daga cikin abin da ya harzuƙa mutane su ka fara ɗaukar doka a hannun su, har da tinzirawar da CBN ya Yi masu, inda ya ce bankunan kasuwanci ne ke ɓoye sabbin kuɗaɗe ba su son bai wa kwastomomin su.

Rabuwar kawuna da saɓani tsakanin Shugaban Ƙasa da Gwamnoni ta yi tsamarin da har wasu sun garzaya Kotun Ƙoli sun maka shi kotu, su na neman kotu ta tilasta wa CBN ci gaba da karɓar tsoffin kuɗaɗe, tunda sabbin ba su wadata ba.

Babban abin tsaro dangane da wannan giribtu da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya yi na hana kuɗaɗe kewayawa a hannun ƙananan yan kasuwa da sauran masu sayen kayan buƙatun yau da kullum, wata illa ce wadda za a daɗe nan gaba ba a magance ta ba.

Tuni har an ma fara hasashen cewa an yi asarar kashi 3 bisa 100 na tattalin arzikin ƙasa a cikin ‘yan kwanakin nan. Kafin canjin kuwa har ana murnar cewa Najeriya za ta samu bunƙasar tattalin arzikin ƙasa da kashi 3.2 bisa 100 a 2023, kamar yadda Bankin Bayar da Lamuni na Duniya, IMF ya yi hasashe.

Abubuwa masu matuƙar hatsari da barazana sun faru kan tattalin arzikin Najeriya da ita kan ta zamantakewar ƙasar, waɗanda kuma barazana ce ga zaɓen 2023.

Idan za a iya tunawa, tun daga lokacin da Emefiele ya tsoma dungulmin yatsun sa cikin siyasa, wannan jarida ta fito ba sau ɗaya ba, ta yi kiran ya sauka daga shugabancin CBN, ko kuma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tsige shi. Kuma tun daga lokacin ne duk mai hangen nesa zai iya fahimtar cewa wannan ɗan ragabza da gidoga bai damu da da kiyaye dokokin aikin sa na shugabancin CBN ba, harankazamar sa kawai ya ke yi, duk kuwa da an san hakan babbar barazana ce ga ƙasar nan.

Saboda haka, Gwamnonin Najeriya sun yi gaskiya da su ka fito a ranar Lahadi su ka ce, “ƙwacen kuɗaɗe Emefiele ya yi wa jama’a, ba canji ko musayar kuɗaɗe ba.”

Tulin kuɗaɗen da ke zagayawa ana hada-hada da su a hannun jama’a, ba su ne ke kawo tsadar kayan masarufi, abinci da tsadar rayuwa ba. Abin da ke tsayar da tsadar farashi shi ne CBN ta gindaya ƙa’ida ko geji na canjin kuɗaɗen waje.

Idan aka kalli yadda masu tarzoma su ka riƙa ragargaza ginin bankuna su na gaggaɓe ƙofofin bankuna ko fasa na’urar ATM wurin neman a maido masu kuɗaɗen su a hannu, hakan ya isa a gane tsarin da Emefiele ya shigo da shi ba mai karɓuwa ko yin tasiri ba ne a cikin jama’a.

Rainin wayo da tunzira jama’a fa Emefiele ya yi, ya ce wai bankunan kasuwanci su ka ɓoye sabbin kuɗaɗe. Amma da ya sha matsa kamar gyaɗa, sai a fito ya faɗi gaskiya, ya ce ba a buga wadatattun sabbin kuɗaɗen da jama’a ke buƙata ba.

Idan aka dubi irin asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi, sai kuma la’akari da halin ƙuncin da miliyoyin mutane ke ciki, babu sauran wata hujja ko dalilin da wani zai kawo domin ya kare wannan wawanci da Emefiele ya ɗibga.

Shin yanzu akwai wani maras kunyar da zai iya fitowa ya kare Emefiele ya ce bai cancanci a tsige shi ba? Tsige Emefiele shi ne alheri kuma yin hakan ne zai zama ruwan kashe dafin gubar da ya dasa a ƙasar nan.

Tags: AbujaCBNHausaLabaraiNewsPREMIUM TIMES
Previous Post

‘Ruhun Mai Tsarki ne ya umarce ni na kashe ta’ – Inji matar da ta kashe ‘yar shekara biyar

Next Post

SITIYARIN TATTALIN ARZIKI: Tinubu, Tallafin Fetur da Amanar Jama’a Kan Siraɗi

Premium Times Hausa

Premium Times Hausa

Next Post
‘Gwamnatin Riƙon Ƙwarya Ko Ihun-ka-banza’

SITIYARIN TATTALIN ARZIKI: Tinubu, Tallafin Fetur da Amanar Jama'a Kan Siraɗi

Discussion about this post

Binciko

No Result
View All Result
Karanta

Ramadan Kareem AD

Sabbin Labarai

  • Yadda ƴan sanda suka kama Ibrahim da ya yi garkuwa da Fatima, ya ƙarɓi kuɗi kuma ya yashe ta a Zariya
  • Kotu ta kori gwamna Sule na Nasarawa, ta ce PDP ce ta yi nasara a zaɓen gwamna
  • Gwamnatin Tinubu ta sanar da dakatar da harajin (VAT) kan man dizal na tsawon watanni 6
  • Matsayar da aka cimma a taron Gwamnatin Tarayya, NUC da TUC – Minista Idris
  • ‘Gyaran Najeriya sai a hankali, miji na ba da rauhanai ya ke aiki ba’ – Remi Tinubu

Abinda masu karatu ke fadi

  • auto verkopen on ZAMFARA: Mahara sun gudu sun bar bindigar harbo jiragen sama a dajin Gumi da Bukkuyum -Inji ‘Yan Sanda
  • Laser-Haarentfernung mit hygienischen Bedingungen und aktuellen Gesundheitsstandards in der Türkei on An yi min murɗiya ne a zaɓen APC, ban yarda ba sai an sake zaɓe – Korafin Bashir Ahmad
  • Call Girls Sehore on Ƙungiya ta yi kira ga gwamnati ta ware kuɗaɗe domin samar da dabarun bada tazarar Iyali
  • buy aged stripe account on Hukumar NBC ta gayyaci mai gabatar da shirin ‘Berekete’, bayan macen da ta kona gashin kan yarinya barkatai, ta sha mari barkatai a hannun sa
  • research and survey on Gwamnan Edo ya bijire wa umarnin kotu, ya ce sai mai shaidar rigakafin korona zai yi sallar jam’i a masallaci

Fanni

Tweets by PTimesHausa
  • All Homepage Blocks
  • Home
  • Home
  • Main Home

© 2023 JNews - Premium WordPress news & magazine theme by Jegtheme.