Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ya bayyana cewa gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ba ta ware ko sisi a kasafin Kuɗin 2023, da sunan biyan tallafin fetur ba.
Kyari ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da ya gana da shugabannin jam’iyyar APC, ƙarƙashin jagorancin Adamu Abdullahi, Shugaban APC na Ƙasa.
“To a shekarar 2022 dai an zuba kuɗin tallafin fetur a kasafin kuɗi. Amma a kasafin 2023, kwata-kwata ba a zuba ko sisi ba da sunan biyan tallafin fetur ba.
“Amma duk da haka sai aka ci gaba da biyan tallafin a cikin 2023 ɗin. Kuma har yanzu NNPCL ta na bin Gwamnatin Tarayya ta bashin naira tiriliyan 2.8 waɗanda har yanzu ba ta biya ba.
Kyari ya ce tallafin mai ya zama tarihi, ya wuce, domin gwamnatin tarayya ba za ta iya ci gaba da biyan kuɗaɗen ba.
Da aka tambaye shi sai yaushe za a kammala gyaran matatun man Najeriya har su koma aiki, sai Kyari ya ce, aikin na tafiya ne daki-daki.
Ya ce za a fara cin moriyar matata ɗaya a ƙarshen 2023, wata ɗaya kuma a cikin 2024 za a kammala gyaran ta.
“Duk kamfanin da aka ce akwai zunzurutun kuɗaɗen sa har Naira tiriliyan 2.8 maƙale a wani wuri, to ina tabbatar maku cewa duk Afrika babu kamfani da zai ɗauki kuɗi ya ba ramce.” Inji Kyari.
Sai dai kuma yayin da Mele Kyari ka jaddada cewa tallafin fetur ya zama tarihi, su kuma shugabannin ƙungiyar ƙwadago (NLC), sun ce ba su yarda da ƙarin kuɗin mai ɗin ba.
Ƙungiyar Ƙwadago ta ce a tilas a soke ƙarin kuɗin mai, an shammaci ‘yan Najeriya.
An tashi taron matsalar ƙarin farashin man fetur tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa baram-baram.
An yi taron a Fadar Shugaban Ƙasa, wanda Shugaban NNPCL, Mele Kyari, hadimin Shugaban Ƙasa Dele Alake, Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta TUC, Festus Osifo da wasu jami’an gwamnati.
Cikin sanarwar da NLC ta fitar bayan tashi daga taron, ta bayyana cewa ita da ‘yan Najeriya ba za su amince da wannan mahaukacin ƙarin kuɗin fetur ba.
NLC ta ce an yi ƙarin ba shiri, kuma an shammaci ‘yan Najeriya da ba-zatar ƙarin fetur.
A ranar Laraba dai NNPCL ta umarci dukkan gidajen mai su koma sayar da fetur daga N480 zuwa N570.
An yi wannan mahaukacin ƙarin ne daga N193 da ake sayarwa a lokacin da aka yi ƙarin.Kakakin NNPCL, Garba Deen Muhammd ya ce ya ce an yi ƙarin kuɗin ne bisa haƙiƙanin yadda kasuwa ta ke a halin yanzu.
NNPCL ta yi sanarwar kwana biyu bayan Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin fetur baki ɗaya a ranar Litinin, lokacin rantsar da shine.
Tuni dai tsohuwar gwamnatin Buhari ta bayyana cewa bai yiwuwa a riƙa biyan tallafin fetur, ganin yadda gwamnati ke kashe naira biliyan 400 duk wata su na tafiyar wajen biyan tallafin fetur.
Dama kuma a cikin kasafin 2023, an tsara cewa batu biyan tallafi tun daga watan Yuni da ya kama yau.
Farkon wannan makon kuma NNPCL ta bayyana cewa ta na bin gwamnatin tarayya bashin naira tiriliyan biyu na kiɗin tallafin da ta biya, amma Najeriya ba ta biya ba, har Buhari ya sauka daga mulki a ranar 29 Ga Mayu.
A na ta bayanin NLC ta ce ya kamata gwamnatin Tinubu ta tuntuɓi ‘yan Najeriya kafin ta yi gaggawar cire tallafin fetur.
Discussion about this post