Tsohon Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika, wanda ya ƙaddamar da Nigeria Air, jirgin holoƙo, ya zargi tsohon Shugaban Kwamitin Majalisar Tarayya kan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Nnolim Nnaji da neman ya ba shi kashi 5% bisa 100 na hannun jarin Nigeria Air.
Sirika ya yi wannan iƙirarin ranar Lahadi, lokacin da ake tattaunawa da shi a Gidan Talbijin na ARISE.
“Nnaji ya tambaye a lokacin da ake buga tandar cinikin hannayen jari cewa ya na so a ba shi kashi 5% bisa 100% na hannayen jarin Nigeria Air, a ba shi wai shi da mutanen sa.” Inji Sirika.
“A wancan lokacin na shaida masa cewa an fara buga tanda, kuma wasu mutane sun saya da daraja. Ina ganin sai dai ka je a wurin su, ka nemi su sayar maka kashi 5% ɗin da ka ke nema.”
Bayanin Sirika ya zo ne ƙasa da sati ɗaya bayan Majalisar Tarayya ta nemi ta binciki harƙallar yadda aka ƙaddamar da jirgin Nigeria Air.
Da ya ke maida raddi kan zargin cewa ya kashe naira bilyan 138 wajen ɗauko hayar jirgin kamfanin Ethiopian Airlines tare da yi masa fenti, Sirika ya ce ƙarya ake yi masa. Ya ce duk mai son Jin abin da aka kashe ai ya na iya zuwa Ma’aikatar Yaɗa Labarai domin samun cikakken bayani.
Shi kuwa Nnaji wanda Sirika ya ce ya nemi a ba shi kashi 5 na hannun jarin Nigeria Air, ya fito ya ƙaryata Sirika, har ya nuna cewa ruwa ne ya ciwo Sirika, sai ya ke ta kame-kamen abin da zai riƙe ya tsira, ko kuma ridar wanda za su bi igiyar ruwa su halaka tare.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin cewa, Majalisar Tarayya ta nemi Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Nigeria Air, a garƙame ‘yan gidogar da su ka ƙaddamar da shi.
Kwamitin Majalisar Tarayya mai lura da Sufurin Jiragen Sama, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta gaggauta soke kamfanin Zirga-zirgar Jiragen Najeriya, Nigeria Air, wanda aka ƙaddamar cikin satin da tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari ya sauka kan mulki.
Kwamitin ya kuma yi kira a gaggauta kamawa tare da garƙame dukkan masu hannu a gidoga da rufa-rufar ƙaddamar da Nigeria Air, wanda majalisa ta ce damfara ce kawai ba wani kamfanin sufurin jirage ba.
An cimma yarjejeniyar amincewa a kira gwamnatin tarayya ta dakatar da Nigeria Air, a lokacin da su ka yi taro da wasu jami’an gwamnati masu ruwa da tsaki a fannin sufurin jiragen sama, a Majalisar Tarayya, Abuja.
Shugaban Kwamiti Nnolim Nnaji, ɗan PDP daga Enugu ne ya karanta matsayar da su ka ɗauka yayin taron.
Waɗanda su ka halarci taron sun haɗa da Ƙungiyar Masu Jiragen Sama ta Najeriya (AON), wakilan Ma’aikatar Harkokin Sufuri ta Ƙasa da sauran su.
Tsohon Ministan Harkokin Sufuri a lokacin mulkin Buhari, wato Hadi Sirika ne ya ƙaddamar da jirgin, wanda daga baya aka haƙƙace cewa holoƙo ne, kuma damfara ce kawai.
Discussion about this post