An bayyana cewa a Najeriya aka fi danne haƙƙin jama’a, idan aka kwatanta da ƙasashen yankin ‘Sub-Saharan Africa’.
Ƙasashen yankin sun ƙunshi Afirka ta Gabas, Afrika ta Tsakiya, Kudancin Afrika da kuma Afrika ta Yamma.
Ƙungiyar Kare Hakkin Jama’a ta HTMI ce ta fitar da wannan rahoton ranar Alhamis, a New Zealand, Hedikwatar da ƙungiyar ta ke.
HRMI ta yi amfani da bayanan da masu rajin kare marasa galihu da ƙungiyoyi ke yi, sai kuma jawaban da waɗanda aka ƙuntata wa ke yi da kan su.
Rahoton ya ƙara da cewa gwamnatoci da suka shuɗe sun kasa cika alƙawarin kare haƙƙoƙin jama’a da su ka ɗauka.
Sannan kuma rahoton ya zargi shugabannin Najeriya cewa ba su ririta arzikin ƙasar, ta yadda za a inganta rayuwar ‘yan ƙasar baki ɗaya.
An ɗora Najeriya kan sikelin samar da abinci, lafiya, ilmi, aiki da gidaje, amma babu wani abin a zo a gani.
Rahoton dai ya ce Najeriya ta fi sauran ƙasashen Afrika lalacewa wajen danne haƙƙin mutane’.
An bayyana cewa a Najeriya aka fi danne haƙƙin jama’a, idan aka kwatanta da ƙasashen yankin ‘Sub-Saharan Africa’.
Ƙasashen yankin sun ƙunshi Afirka ta Gabas, Afrika ta Tsakiya, Kudancin Afrika da kuma Afrika ta Yamma.
Ƙungiyar Kare Hakkin Jama’a ta HTMI ce ta fitar da wannan rahoton ranar Alhamis, a New Zealand, Hedikwatar da ƙungiyar ta ke.
HRMI ta yi amfani da bayanan da masu rajin kare marasa galihu da ƙungiyoyi ke yi, sai kuma jawaban da waɗanda aka ƙuntata wa ke yi da kan su.
Rahoton ya ƙara da cewa gwamnatoci da suka shuɗe sun kasa cika alƙawarin kare haƙƙoƙin jama’a da su ka ɗauka.
Sannan kuma rahoton ya zargi shugabannin Najeriya cewa ba su ririta arzikin ƙasar, ta yadda za a inganta rayuwar ‘yan ƙasar baki ɗaya.
Discussion about this post