Shugaban Gidauniyar Bill and Melinda, Bill Gates, ya yi matukar nuna damuwa ganin yadda Gwamnati ba ta ɗaukar kiwon lafiya da muhimmanci ga ‘yan Najeriya.
Bill Gates ya yi wannan ƙorafi ne ranar Laraba a Legas, lokacin da ya ke jawabi a Taron Inganta Rayuwar Matasa Masu Fasahar Ƙirƙira, a ranar Laraba.
Ya ce dala 10 kacal Najeriya ke kashewa a duk shekara kan kowane mutum ɗaya a fannin lafiya.
Dala 10 daidai ta ke da Naira 6,900 a kasuwar ‘yan canji a ranar Laraba.
Ya ce ganin yadda Najeriya ke cike da matasa masu basira, ya zama dole gwamnati ta tashi tsaye wajen ƙara yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa a fannin kiwon lafiya.
“Abin zai ba ku mamaki idan ku ka ji cewa dala 10 kacal Najeriya ke kashe wa kowane mutum ɗaya a duk shekara, amma ƙasashen Saharar Afirka na kashe har dala 31.
Ya ce matasa ne tubali da ginshikin gina ƙasashe. Don haka kada Najeriya ta yi wasa da na ta matasan.
Ya tabbatar cewa Naira 6,700 kacal gwamnatin Najeriya ke kashe wa kowane ɗan ƙasa a kiwon lafiya.
Shugaban Gidauniyar Bill and Melinda, Bill Gates, ya yi matukar nuna damuwa ganin yadda Gwamnati ba ta ɗaukar kiwon lafiya da muhimmanci ga ‘yan Najeriya.
Bill Gates ya yi wannan ƙorafi ne ranar Laraba a Legas, lokacin da ya ke jawabi a Taron Inganta Rayuwar Matasa Masu Fasahar Ƙirƙira, a ranar Laraba.
Ya ce dala 10 kacal Najeriya ke kashewa a duk shekara kan kowane mutum ɗaya a fannin lafiya.
Dala 10 daidai ta ke da Naira 6,900 a kasuwar ‘yan canji a ranar Laraba.
Ya ce ganin yadda Najeriya ke cike da matasa masu basira, ya zama dole gwamnati ta tashi tsaye wajen ƙara yawan kuɗaɗen da ta ke kashewa a fannin kiwon lafiya.
“Abin zai ba ku mamaki idan ku ka ji cewa dala 10 kacal Najeriya ke kashe wa kowane mutum ɗaya a duk shekara, amma ƙasashen Saharar Afirka na kashe har dala 31.
Ya ce matasa ne tubali da ginshikin gina ƙasashe. Don haka kada Najeriya ta yi wasa da na ta matasan.
Discussion about this post